WAYON ACI, WAI AN KORI KARE… 3

0
8238

WAYON ACI, WAI AN KORI KARE DAGA GINDIN ‘DINYA (3)

A gidan masu kudi kuwa da yawa daga cikinsu kusan da kyar su ke son rabuwa da ‘ya’yansu mata ba komai girmansu kuwa. Kuma wai don ‘ya’yansu mata balagaggu su uku ko hudu sun tare a gabansu babu wacca ta yi aure, kalilan ne za ka ga sun damu da hakan. Sannan in har wani dalili ya sa aka sako ta, daki za a share mata, a yi masa sabon fenti, a sake mata gado da katifa, labulaye da sauransu don ta samu gindin zama durshen ta ci karenta ba babbaka a gidansu. In mijin ya zo ayi masa tas, har ta uwa, ta uba.

Ba sau daya ba ba sau biyu ba akan samu matar mutum ‘yar masu boza in an aureta ya zamana kullu-yaumun sai ta je gidansu ta kusan yini, wani lokaci in ta ga dama har ta kwana ko ta yi kwana da kwanaki. Ko kuma kawai a aiko da bada fasfo za a yi mata bizar tafiya kasar waje yawon shaqatawa ko da kuwa mijin bai amince ba. In kuwa ya nemi ya kawo cikas sai su ce ba dole ba ne ya saketa in ya ga ba zai iya ba. In kuwa har ya saketan, toh ko d’is a jikinsu.

Sai kawai su sa ta koma gida ta ci gaba da sha’aninta da sauran kannenta tumatuma a gaban iyayen. Bayan wani dan lokaci don kar ‘yan uwa su sa mata idon ko wani ko wata daga dangi ya damesu da daurewa matar gindin zama don kuwa ai yanzu ba yarinya ba ce, sai su sa ta ta koma makaranta ko a nan gida Najeriya ko su tura ta ‘kasar waje don yin digirgir dinta. Zancen aure kam babu shi. Yara in ta haifa ace wa ubansu ya zo ya kwashesu in bata so. In kuwa ta na son kayanta, sai iyayenta su riqesu a wajensu.

Toh yanzu in har aka kafa wannan doka ta hana qarin aure ga mai karamin qarfin don gudun haihuwar yara barkatai wadanda iyaye marasa galihu kan turo su cikin gari daga kauyuka da karkara yin almajiranci saboda ba su da sukunin daukan nauyinsu na  ciyarwa, tufatarwa, ilimantarwa, tarbiyantarwa da dai makamantansu, wa da wa abin zai shafa kai tsaye? Na daya dai karara kowa ya san talakawa iyeyen ‘yammata nan da akan aurar su na shekaru 15, 16, 17 abin da ya yi sama su wannan doka za ta soma bari da rida-ridan, balagaggun ‘yammata a gabansu. Su kuma rasa yadda za su yi da su.

Na biyu kuma su kansu ‘yammatan wannan doka za ta shafesu ba kadan ba. Ba don komai sai don saboda rashin sukunin iyaye yarinya ta kan yi saurin yarda ta yi aure ko don ta sauwaqewa iyayenta dawainiyarta, banda sake da walwalar da kan biyo bayan samun waje na ta na kanta don ci gaba da gudar da rayuwa. Domin in hakan ba ta samu ba, toh a matsayinta na matashiya mai danyen jini a jika, ga kuruciya ga sha’awa ya nai mata ‘kaimi, toh fa in ba namiji ta samu ba a sunnance, tabbas za ta yarjewa wani a fasiqance. Abin kuwa da zai biyo baya ba sai an yi wani bayani ba.

Da zarar an shaidi cewa wannan budurwa ta san d’a namiji har ta kai ga yin cikin shege, ko da an zubar da cikin fa, an riga an yi mata lamba. Duk wani namiji wanda ya ke son zuriyya dayyiba toh da wahala ya ce zai yarda ya auri wannan yarinya. Ka ga in ta kasance akwai ‘kannen irin wannan budurwa biyu ko uku duk su na biye da ita, cikin dan lokaci kankani za su isa aure, kuma uban nan na su ya rasa yadda zai yi da su tunda ba su kai shekarun da aka kayyade cewa shine mafi karanci na ayi mu su aure ba.

ALMAJIRI PHENOMENONTo mu bar shi ma ta farkon ta kai shekaru 18, sai aka samu akasi ba ta samu miji da wuri ba har qanwarta ta zo ta kai shekarun aure da doka ta gindaya, ita kuma sai ta samu wani ta na son sa amma ya na da mata kuma ba shi da karfi sosai amma ya na da d’an rufin asiri daidai gwargwado ba laifi, zai iya daukar nauyinta amma ba yadda dokar ta ke so ba, sai aka hana shi aurenta. Bayan shekara ita kuma ta ukun ta kawo karfi, nan kuma bacin ta samu mai aurenta sai ta kasance matansa biyu yaransa goma, nan ma sai aka ce a’a sai dai du su haqura, toh yaya mahaifin wadannan ‘yammata zai yi, ga shi ba shi da wadatar ci gaba da ajiyesu?

Kar fa a manta da cewa akwai samari ‘yan ta more, ma su hurewa ‘yammata kunne da yawa a cikin gari su na kai kawo don su sami wata ta matsu su rafke ta. Ga ‘yammata sun soma zama manya mata a gidajen iyayensu babu aure su wajen 4-6 in an had’a da zawarawan da su ka yi aure rashin jituwa ya kawo rabuwa. Shin wannan uba yaya zai yi da wadannan ‘yammata, manyan mata da kuma zawarawa a gidansa? Shin zai iya daukar nauyinsu baki daya, ga shi doka ta hana shi aurar da su ga mazaje masoyansu da aure? Wane tallafi za’a ba shi don tabbatar da cewa gidansa bai gagare shi ba?

Su kuma wadannan ‘yammata, kwanannun mata da zawarawan yaya za a yi da sha’awarsu ta d’a namiji da ke kaikawo a jikinsu? Ko azumi za a tilasta musu su dinga yi ala ayya hallin har su samu mazajen aure? Duk wacca ta samu miji amma aka ce mijin da sauransa wajen cika sharuddan hukuma, aka hana su auren ya za su yi da kansu? In kuma aka samu wasu sun yi zina har sun samu juna biyu, wane tanadi hukuma ta yi na sarrafa wannan aika-aika? Uban za’a kama ko ‘yar ko wanda ta ce shi ne don kawai ta na sonsa alhali mazajen da su ke kwanciya da ita su fi biyu? Bulala za ayi ko kisa?

Kai duk wannan ba ita ce ma matsalar ba. Babbar matsalar anan ita ce in ire-iren wadannan mata su ka haura shekaru arba’in (40) zuwa hamsin (50) ba su yi auren fari ba, alhali ba rasa auren su ka yi, a’a doka ce ta hana su saboda ka’idojin da aka gindaya sun yi tsauri da yawa, yaya za’a yi da haqqoqinsu? Don kuwa wannan al’amari kasashen larabawa irinsu Saudiya, Misra, Maroko, Kuwait, Qatar da dai sauransu da su ka assasa irin wadannan dokoki su na nan su na fama da wadannan qalubale, sun kuma rasa yadda za su yi da al’amarin.

Akwai labarai da dama wadanda ake yadawa cewa wasu daga cikin irin wadannan ‘yammatan a gidajen masu hannu da shuni da dokar kasa ta hana su aure ko zaman aure, iyayensu maza wato kawunninsu, baffaninsu, ‘ya’yan yayyen ko qannen uba ko uwa, ma su gadin gida, direbobi, ma su yi mu su hidindimu daban-daban maza da dai sauransu su ne su kan biya mu su buqatun na saduwa duk sanda dama ta samu.

Sannan akwai matasa irin ‘yan Kano tu Jiddan nan da su ka ce larabawa kan dauki hayan zaratan karti su kai su gidajensu don saduwa da ire-iren wadannan kwantain mata, a kuma biya wadannansamarin kudin aikata wannan masha’a. Allahu A’lam.

Toh bari kuma ku ji wata sabuwa ful. In an lura da kyau za’a ga cewa yawanci mata da su ke da matsalar aure, ba ‘ya’ya ko mata ko zawarawan da iyayensu su ka kasance talakawa ba ne. Su kam cikin dan lokaci qanqane za ka ji ana shelar daurin aurensu. Amma ‘ya’yan mawadata fa? Sai dai jifa-jifa za ka ji zancen auren wata daga cikinsu. Kuma duk inda aka aurar da guda daya, toh sai a yi shekara da shekaru da dama ba’a sake aurar da wata a gidan ba. Sau da dama za ka samu akwai matan da su ka kai shekaru kusan arba’in ko ma fiye ba su yi auren fari ba a irin manya-manyan gidajen nan.

Yanzu idan aka hana mai karamin karfi aure ko kara auren yarinyar da ya ke so ta ke sonsa, ko a hana mai mace daya qara ta biyu zuwa sama, sannan a ce bazawara ba za ta auri wani ba don hukuma na ganin ba shi da jarin gudanar da zamanta a gidansa, me a ke zaton zai kunno kai? Daga cikin annobar da za ta samo wanzuwa a cikin al’umma ita ce yawan zinace-zinace ne zai qaru, yin cikin shege ya biyo baya. Kowa kuwa ya san duk al’ummar da zina ta zame mata ruwan dare, ita kam wannan al’umma kashinta ya bushe.

Ba ya da wannan fa mata ne za su shiga daukar nauyin kansu don samawa kansu mazajen aure. Sai ka ga mace ta yarda tsakaninta da namijin da ta ke so, ta amince ma sa kawai ya yarda zai aureta, ita kuma za ta dau dawainiyar ci da kanta, tufatar da kanta, ta kama musu gidan haya, ta kula da lafiyarta, ta dau dawainiyar ‘ya’yansu da dai dukkanin abinda aka ce mijine zai tanadar. Ka ga in har matar ta ce ta ji ta gani babu mishkila, wace hukuma ce za ta hana wannan aure? Toh, tambaya anan ita ce su wa da waye za su iya aiwatar da wannan a cikin al’umma? Talakawa ne ko ma su wadata ko mata ‘yan boko?

Kun ga daga mata ma’aikata ma su samun albashi duk wata, sai kuma ‘ya’yan ma su kudi da iyayen yarinya a duk wata za su turawa ‘yarsu kayan abinci da kuma alawus cikin asusun ajiyarta na banki duk wata, kakarsu ta yanke saqa ke nan. Kun ga in dai matar ba ta kai qorafi ba, ai zancen mijinta ya kasa ko ya gaza ba ta haqqoqinta bai ta so ba. Duk wanda ya iya allonsa kuwa sai ta kasance ya na da mata har hudu cifcif ba tare da ana jin kansu ba. Yau yana gidan wannan ma’aikaciyar baki, gobe yana tare da wata likitar asibiti, jibi ya koma wajen wata ma’aikaciya shari’a, gata kuwa ya sha gata a wajen wata ma’aikaciya gwamnati.

Toh, kun ji inda taken wannan rubutu ya samo asali ke nan. Wato dai “Wayon aci ne, wai an kori kare daga gindin dinya.” ko ba haka ba. Talakawa doka ta hana su auren halal, su kuwa mawadata su aurar da kwantan ‘ya’yansu, su kuma tallafawa mazajen wajen cimaka da kayan sarrafa auren ‘ya’yan na su. Ko kuma duk ‘yarinyar da ta yi boko ta ke aiki ta na karbar albashi duk wata ta ce ‘e’ ta ji ta gani, ta yarda za ta auri mijinta ta kuma dauke masa dukkan wani nauyin aure da ya rataya a wuyansa. Kun ga mafi akasarin ridaridan matan da ba su da aure a gidajen mawadata da kuma wadanda karatun boko ya kawo mu su cikas wajen yin aure, wannan kyama za ta kaurace mu su.

Su kuwa ‘ya’yan talakawa da iyayensu, su je su can su yi ta zinace-zinacen su doka ta gille mu su damar yin auren sunnah. Ka ga reshe ya juye da mujiya ke nan. An nemi tsaftace zaluncin da ake yiwa mata, amma an kuma don kuwa ba’a rabu da Bukar ba wai an haifi Habu. Daga baya mata, ‘ya’yan talakawa ne za su shiga cikin mawuyacin hali don za su zo su ka kama lamuntar duk irin wulaqanci da zaluncin da mazajen su za su shiga yi mu su saboda gudun kada mazajen su sake su. Ka ga duk abin ya koma gidan jiya ke nan. Sai ma abinda ya qaru kawai.

Aah sai abinda ya qaru mana don da ai ‘ya’yan halal, ‘ya’yan sunnah ne ake haihuwa a cikin al’umma illa dai rashin kulawa da ba su haqqoqinsu na rayuwar yau da kullum, in da za ka ga iyayen sun yi biris da al’amarinsu amma ba su daina hayayyafosu ba. Amma in wannan doka ta kafu kuma ta kankama toh fa daya daga matsalolin da ka iya biyowa baya shige yara maras iyaye ne wato shegu, ‘ya’yan zina ne za su cika garin ta ko’ina. Sannan kuma in ba kyakkyawan shiri hukuma ta yi ba don ta tsara yadda za’a sarrafa rayuwar irin wadannan ‘ya’ya marasa iyaye maza ba, sai abin ya fi na almajirai muni.

Ka ga maza zasu kama za6an mata su darje ke nan. Don waye zai yadda ayi masa bulala 30, ga tara na wasu dubbani nairori sannan kuma har ta kai ga dauri a gidan kaso? A’a wAllahi. Kawai mutum ya bi lamuransa sannu a hankali, ya nemi mace mai dukiya ko ‘yar gidan mawadata, fara tas da ita, kyakkyawar gaske, doguwa santaleliya mai gashi har gadon baya, ga abinci ta samar, ga gida na gani na fad’a mai esi da jakuzi.

Dori akan wannan ga mota dandasheshiya, ba ruwan mutum da kudin mai balle na sabis, kuma ba kala daya ba ba biyu ba, kawai ka shiga abinka ka kutsa duk inda ka ke son. In ka ji kiran sallah ka paka ka fito ayi jam’i da kai. Daga nan ka sake shiga sabuwar yayi, ka daga gilasai ma su duhun wato an sa mu su tintet, ka kunna ra6a, ka sa sautin mai ratsa jiki ka na jin kayanka sauwa-sauwa sannan ka lalubo baqin tabaronka ka maqala, ka zauna a gefen duwawunka ka bazama cikin gari sai inda jar wutar bada hannu taima tsaiko.

Ni dai abinda na hango ke nan. Amma za ta iya kasancewa ban hango daidai ba. In ta kasance haka toh, mutum ajizi ne tara ya ke bai cika goma ba. Sai dai zai yi wahala ace hakan ba ta kasance ba. Duniya ce fa. Daga ganin yadda abubuwa su ke gudana da inda ta dosa, hasashen yanayi na nuna cewa komai na iya faruwa. Juma’ar da za ta kyau, daga laraba ake gane ta, in ji ma su iya magana. Bari dai in bar zancen a haka. Sai wani jiqon kuma.

(c)2017 DesignWorld INT’L/SWS.Comms

A Kiyaye Dukkan haqqin Mallaka

https://web.facebook.com/DWinternational/

Comments

comments