A QARNI NA 21, SHIN WAI WAYE MALAM BAHAUSHE NE?

0
190 views

A QARNI NA 21, SHIN WAI WAYE MALAM BAHAUSHE NE?Image result for Bahaushe

Marubuci: Tijjani Muhammad Musa

Da mu ke yara, akwai wani al’amari da na lura da shi wanda yanzu haka ya yi qaranci ainun. Kusanma nema ya ke ya shiga kundin tarihi. Dalilin da ya sa hakan na ke kokarin ganowa.

Sana’o’in da mu ka gada kaka da kakanni wadanda aka san mu, iyayenmu, gidajenmu, anguwanninmu da ma al’umarmu da su duk mun watsar, mun dauki girman kai mun maye gurbinsu da shi.

Wanda wadannan al’amura ba karamin tasiri su ke da shi wajen shedawa duniya ko mu su wanene a jinsin bani Adama ba. Don kuwa a duk fadin duniya nan babu wasu mutane ma su yin wadannan harkokin rayuwa idan ba Hausawa ba.

A sana’ar maza akwai noma, farauta, su, qira, saqa, jima, rini, dinkin kaya da huluna, dukanci, kasuwanci, fatauci da dai sauransu. Wasu kuma za ka same su su na malanta, fawa, gwari, gini, gyartai da makamantan wadannan aiyukanmu na gargajiya.

Mata kuwa su ke yin sana’ar abincin sayarwa da abin sha iri-iri. Sannan ka samesu su na kiwo, dillanci, saqa, kitso, kunshi, yin man quli, man shafawa, qulle-qullen kayan miya, surfe, niqa, wanki, wanke-wanke da makantansu.

Hakan ta sa wasu daga kusa da ma nesa wadanda wani dalili walau na ‘yan uwantaka, zumunci, kasuwanci, fatauci, neman ilimi, yawon buda ido da dai sauransu kan yi mamakin halayyarmu, dabi’unmu da al’adarmu har ta kai su na sha’awar koyi da mu.

Bayan anyi kyakkyawar mu’amala da wadannan baqi na wani dan lokaci, sun ci, sun sha, sun ji kuma sun ganewa idanuwansu yadda Bahaushe ya ke gudanar da rayuwarsa cikin yarda, aminci, karamci da kyautatuwa abokan hulda, su kan yi ma sa kyakkyawan shaida bayan rabuwa.

Bacin kowa ya koma gida wato garinsu, ya kan ba da labarin irin yadda Malam Bahaushe ya ke, tare da kwadaitawa duk wanda ya saurare shi da shima ya je Kasar Hausa ya ganewa kansa wadannan mutane ma su kyan dabi’u da haba-haba da baqi.

Toh, ma su iya magana su kan ce “Idan mutum ya na da kyau,to ya qara da wanka.” Sai dai fa kash, a gaskiya mu na sakaci wajen kyautata kyawawan halayenmu da wasu su ke sha’awarmu ta dalilinsu. Inda za ka ga babu wani kokari na mu a al’ummance ko a gwamnatance don tallata Hausawa a idon duniya.

Yanzu zamani ya zo da wani yanayi na yad’a bayanai ga duniya ta wata sabuwar fasahar zamani dangane da asali, al’adu, tarihi, rayuwa, addini da ire-iren ci gaba ko akasin hakan da al’uma su ke da shi, ko su ke burin samawa kansu. Ina ake cin nasara, ina ake samun qalubale? Su wa da su waye ke rawar takawa don a cimma buri?

Image result for Bahaushe

Duniya yanzu lungu da saqo musamman ma a kasashen da su ka yi fice wajen tattalin arziqi, ilimi, kimaya da fasaha, adabi, yada al’adun gargajiya da sauran fannonin ci gaban rayuwar dan Adam musamman kasar Amurka da kasashen Turai irinsu Ingila, Faransa, Jamus, Kasar Chaina da sauransu duk suna sha’awar sanin wai shin waye Bahaushe ne? Ko menene dalili?

Tambayar da zan yi anan ita ce, idan ni mai sha’awar son sanin Bahaushen mutum ne, ba don komai ba sai kawai don shahara da tasirin da harshen Hausa ya yi, har ta kai fitattun kafafen yad’a labarai na duniya na amfani da shi wajen gabatar da shirye-shiryensu, waye ya fi dacewa ya biya mun wannan buqata? Bahaushe ko wani wanda ya kawo ziyara kasar Hausa?

Sannan kowa ya san yanzu haka hukumar gudanar da dandalin sada zumunta na Fesbuk mai mambobi fiye miliyan dubu daya da maitan ta amince da amfani da harshen Hausa cikin jerin gwanon fitattun yarukan duniya irinsu Turanci, Larabci. Faransanci, Jamusanci da dai sauransu da ma’abota hawa wannan fage za su iya za6a don gudanar da musayan bayanai a wannan sabuwar kafar sadarwa ta zamani wato intanet. Ko me ya kawo irin wannan karbuwa?

Baya da wannan, ace wani ya samu labarin dadadden tarihin Kano da masarautarta da ma wasu cikin yankin Arewa da ake wa jimla da sunan Kasar Hausa. Wai ya ji an ce wannan gari ‘Ta Dabo jalla babbar Hausa’ ya fi shekaru 1000 da doriya da kafuwa?

Wannan mabuqaci kuma ya nemi sanin yadda mutanen wannan waje ke rayuwa a gargajiyance, a rubuce ta kafar yanar gizo don neman ilimi, ko niyyar zuwa yawon buda ido, shin zai sa mu bayanai tiryan tiryan kamar yadda ya kamata kuwa?

Image result for Bahaushe

Ku na ganin su waye ya fi cancanta su gaya ma sa, su gayawa duniya halayya, dabi’u, al’adunmu na gargajiya fiye da mu kanmu?

Tabbas kam, babu wanda ya wuce Bahaushe ko Bahaushiya. Da yawa al’umar duniya a bangarori daban-daban, a fannonin rayuwa kala-kala su na neman sahihan bayanai daga tushe, daga tsatso wato asalin abin, Hausawa ke nan.

Ya kamata mu sani, in fa ba mu tashi tsaye mun duqufa wajen rubuce-rubuce a dukkan fannonin rayuwar Malam Bahaushe ba, toh wasu ne za su ci gaba da yad’a bayanai

na boge, na jabu, na qarya da shaci-fadi da dai sauransu dangane da ko waye Bahaushen mutum da al’adunsa. Wanda hakan kuwa ba qazamar illa zai yi wa Hausawa a idon duniya ba.

Sannan wajen tabbatar da wannan al’amari ya kamata gwamnati, masarauta, jami’o’i, kafofin sadarwa, marubuta, mawaqa, ‘yan fina-finan Hausa, kungiyoyi masu zaman kansu, masana harkar intanet, kwararru a harkar yawon bude-ido, attajirai, ‘yan kasuwa, mutanen gari na karkara da na birane, masoya Arewa da Hausawa a taru a yi wani jadawalin cimma wannan gagarumin fidda jaki daga duma.

Da nan ba da dad’ewa ba Malam Bahaushe ya yi sakaci, wajen harkar jarida, yada labarai, fadin ra’ayinsa da matsayinsa dangane da dukkan lamuran da su ka shafe shi a Kasar nan da ma duniya baki daya. Inda ma su harka da adabi, marubuta, ‘yan jarida, kafafen yada labarai a kudancin kasarnan da yammaci duniya su ke da hanyoyi da kafafen isar da sakqonni, bayanai ra’ayi iri-iri, kuma su ke amfani da su wajen fadin dukkan abinda su ka ga dama na gaskiya ko na qarya musamman na qaryan game da Bahaushe mutum.

A QARNI NA 21, SHIN WAI WAYE MALAM BAHAUSHE NE?
Bahaushe

Amma yanzu wata damar ta sake samuwa inda kowa ya tsinci kansa a ga6ar mafari. Wato da ‘yan kudu da ‘yan arewacin Najeriya duk an dawo an sake lale, an kuma daidaita sahu don sake yi tseren koya da kuma kakkafa kafafen yada labarai irinsu jaridu, mujallu, gidajen radiyo da na talabijin da aka sani tun fil azim da kuma wasu sabbin hanyoyin sadarwa a zamanance irinsu shafukan yada bayanai, labarai, hotuna da bidiyo duk a lokaci guda kuma a kafa guda, cikin sauqi, sauri, inganci sannan a farashi dan qalilan.

Wato wata fasaha ce da zamani ya zo da ita wacca kowa zai iya amfani da ita ya gayawa wa duniya haqiqanin gaskiyar lamari akan komai, kuma game da kowa. Sannan ba ta da wata dawainiya ko tsadar da aka sani ke yi wa dukkan kokarin sadar da saqonni ya isa ga dumbin jama’a cikas ko tarnaqi. Wanda hakan ba qaramin tasiri ya ke da shi wajen daqushe malam  Bahaushe ba, in har ya qudiri niyyar yada labarai da rahotanni, ra’ayi, al’adu ko adabinsa ga sauran al’umar duniya.

Dadindadawa, ba kawai a rubuce ba, harma ta hanyar daukan hotuna don ganewa idanu kawai ba, mutum zai iya yin majigi wato bidiyo don nunawa duniya qarara yadda dukkan al’amuranmu ke gudana akan komai. Wannan fa ba mu na nufin yin fina-finanmu na Hausa da akan yi amfani da su wajen tallata al’adar jinsi ba.

Ta wannan sigar intanet yanzu ba kawai sai kwararru ba, kusan duk wani mai na’urar sadarwa ta wayar hannu, wato salula ke nan muddun dai wayar za ta iya hawa yanar gizo, zai iya daukan hoto ko bidiyon abinda ke faruwa a ko’ina, kuma nan take ya yadawa duniya. Ko ya shigar da abinda ya tattara cikin na’ura mai kwakwalwa wato komfuta ya aika wa duniya ta kafar intanet.

Musammamma in har zai iya yin bayani ko ya yi rahoto ko sharhi bisa doron ilimi da masaniya akan hoto ko bidiyon da ya samar, toh ya yi hakan cikin harshen Hausa, ba sai lallai da Turanci ba. Duk da shike a gaskiya da za’a samu yin bayanan cikin harshe nasara da abin zai fi sauri samun fahimta da kuma sauqin yaduwa a duniya. In kuma da akwai dama toh ayi bayanan cikin harsuna guda biyun.

Image result for Hausawa

Kun ga yanzu zancen wasu sun fi wasu samun dama ko hanyar yada labarai duk ta kau. Wanda hakan ya na daga cikin dalilan da yan Arewa ke kokawa dangane da bayyana ra’ayin akan abubuwan da ke gudana a kasarmu. Yanzu kowa na da dama cikin sauqi ya gayawa duniya abin da ake ciki akan komai na rayuwar al’ummarsa. Da dai an yi wa Malam Bahaushe fintinkau wajen mallaka da kuma yada labarai ta kafofi daban-daban amma ban da yanzu.

Sannan kar a manta da fassara kusan komai na ilimi don ci gaban Malam Bahaushe da mutum ya tsinta, ya samu, ya koya, ya gano ko ya fahimta a duk inda dama ta samu wato a karance-karance, a makarantu, wajen yin bita, taron karawa juna ilimi, a yanar gizo da dai sauransu. Yin haka ba qaramin budawa al’umarmu fahimtar daga ina duniya ta taho, a ina ta ke, sannan ina ta dosa ba. Ka ga ba tare da bata lokaci ba, sai kawai mu dafewa jirgin a tafi da mu.

Ta hanyar amfani da intanet ya kamata al’umarmu maza da mata kowa ya tashi tsaye don yin bayanai, rubuce-rubuce, daukan hotuna, yin majigin da dai sauransu akan Malam Bahaushe. Shi waye shi? Me ya ke so, me ya ke kyama? Ya ya rayuwarsa ta ke kuma ya ya lamarin siyasarsa, addininsa, ilimisa, sana’arsa, mu’amalarsa da dai sauransu su ke? Ba don komai ba sai don shayar da duniya kishir ruwa da kuma ciyar da ita yunwar da ta ke da ita game sanin tarihi, halayya, rayuwa da kuma al’adun gargajiya na “…mai ban haushi, na Tanko mai kan bashi.”

Kar kuma kowa ya yi kasa a gwuiwa, musamman wadanda su ka iya karatu da rubutu a harsuna daban-daban, ya kamata a duqufa wajen qirqiro shafuka (pages), matattara (groups) kafofin sada zumunta (social media) da dandaloli (websites) akan komai dangane da Malam Bahaushe da al’adarsa. Duniya ta ji daga bakin mai ita, ba na ji an ce ya ce ta ce ba.

Ku sani cewa duniya na nan na jiran ta ji daga bakinku amsar tambayar ta “Shin, wai waye Bahaushe mutum ne?” Ko dai ku gaya ma ta da kan ku, ko wasu da ba su san komai game da ku ba, su gayawa duniya ko ku su wanene. Kuma ba lallai ba ne su fada ma ta gaskiya ba, ko su yi mu ku adalci ba.

Wasunmu dai sun dau hanya. Duk mai sha’awar ayi da shi, toh ya qudiri niyya, ya daure kayansa, ya kuma daura damara. Sannan ya same mu a hanya.

(c) 2017 Tijjani M. M.

A kiyayi dukkan haqin mallaka

https://web.facebook.com/DWinternational/

 

 

58 total views, 1 views today

Comments

comments

Previous articleBIO RHYTHMMAA (poem)
Next articleTEE TALK WITH… TINIKA
DesignWorld INTERNATIONAL "It's All About You" is an Online Magazine on INFORMATION, EDUCATION, ENLIGHTENMENT & ADVERTISING. DesignWorld INTERNATIONAL (DWi) from the stables of SOUNDWORD & SIGHTS COMMUNICATIONS LIMITED is an online Advertising Magazine with the slogan “It’s All About YOU”, specially packaged to advertise you, your products and your services on its carefully designed pages. OUR MISSION: To tell your customers and the global village about you, who you are, what you do, why you do what you do, where you are located and when you are available for business, online and offline.