Home HAUSA

HAUSA

Mahabun da kasancewa da Sashen Hausa na mujallar DesignWorld INTERNATIONAL.

A wannan bangare za’a samu rubuce, rubuce, hotuna, sautika, majigi ko bidiyo, labarai da rahotanni, da dukkan abinda ya shafi ji, gani ko kuma sanin dukkan al’amuran da su ka shafi rayuwar dan Adam.

Dukkan wadannan abubuwan kuwa za su samo asali ne daga mutane daban-daban kuma daga ko’ina a duniya.

Mu nai mu ku lale, marhabun…

A QARNI NA 21, SHIN WAI WAYE MALAM BAHAUSHE NE?

0
Sannan kowa ya san yanzu haka hukumar gudanar da dandalin sada zumunta na Fesbuk mai mambobi fiye miliyan dubu daya da maitan ta amince da amfani da harshen Hausa cikin jerin gwanon fitattun yarukan duniya irinsu Turanci, Larabci. Faransanci, Jamusanci da dai sauransu da ma'abota hawa wannan fage za su iya za6a don gudanar da musayan bayanai a wannan sabuwar kafar sadarwa ta zamani wato intanet. Ko me ya kawo irin wannan karbuwa?

DALILIN SAKE-SAKEN AUREN MALAM BAHAUSHE (2)

0
Shi ya sa za ka ga a rayuwar wasu qabilun, wai don namiji magidanci ya na yin zinace-zinace, toh fa ba wani dalili ne na a zo a gani ba, ko na tada jijiyar wuya , ko na neman a zo ace za'a yi ma sa Allah wadai ba. A'a kusan ma abin ya zama abin kwalliya a gare shi. Ku san ma in ba shi da farka a waje, wato matarsa ce kawai ta ke sanin tsiraicinsa, toh fa shi da sauransa a zama gawurtaccen namiji.

DALILIN SAKE-SAKEN AUREN MALAM BAHAUSHE (1)

0
Da farko cewa ya yi kowa ya san malam Bahaushe idan ya yi aure, toh, in ba fasiqi ne shi, mai wasa da addininsa, maras tsoron Allah toh da wahala ka same shi ya na neman matan banza a waje. Sau da yawa ya kan ke6e kansa dangane da buqatunsa na saduwa da mace ga matarsa ta sunnah kawai.

WAYON ACI, WAI AN KORI KARE… 3

0
Akwai labarai da dama wadanda ake yadawa cewa wasu daga cikin irin wadannan 'yammatan a gidajen masu hannu da shuni da dokar kasa ta hana su aure ko zaman aure, iyayensu maza wato kawunninsu, baffaninsu, 'ya'yan yayyen ko qannen uba ko uwa, ma su gadin gida, direbobi, ma su yi mu su hidindimu daban-daban maza da dai sauransu su ne su kan biya mu su buqatun na saduwa duk sanda dama ta samu.

WAYON ACI, WAI AN KORI KARE… 2

0
Sai dai kash wannan tsarin ya samu akasin cin karo da tsarin neman ilimin boko ga 'ya mace. Shi ilimin boko an shirya shi ne daki-daki kusan kusan kashi biyar, in an hada da rukunin farko na yaran da ba'a dad'e da yaye su daga sha nono ba wato abinda turawa ke cewa Nazare, inda yara kan yi shekara daya zuwa biyu a cikinsa.

WAYON ACI, WAI AN KORI KARE…

0
To mu bar shi ma ta farkon ta kai shekaru 18, sai aka samu akasi ba ta samu miji da wuri ba har qanwarta ta zo ta kai shekarun aure da doka ta gindaya, ita kuma sai ta samu wani ta na son sa amma ya na da mata kuma ba shi da karfi sosai amma ya na da d'an rufin asiri daidai gwargwado ba laifi, zai iya daukar nauyinta amma ba yadda dokar ta ke so ba, sai aka hana shi aurenta. Bayan shekara ita kuma ta ukun ta kawo karfi, nan kuma bacin ta samu mai aurenta sai ta kasance matansa biyu yaransa goma, nan ma sai aka ce a'a sai dai du su haqura, toh yaya mahaifin wadannan 'yammata zai yi, ga shi ba shi da wadatar ci gaba da ajiyesu?

DILLALAN FILAYE A ABUJA SUN KOKA

0
Rahoton Ibrahim Babangida Surajo Sana’ar dillancin filaye a birnin tarayya Abuja tana daya daga cikin sana’o'in da su ke garawa a ‘yan shekarun baya baya...

KYAKKYAWAR BUDURWA MAI GEMU…

0
Harnaam Kaur, ‘yar asalin kasar Birtaniya, wadda take da yawan gashin fuska kamar namiji, ta bayyanar da labarinta, a matsayin wani abun da ta sha wahala, domin kuwa idan aka ganta da gemu da gashin baki, sai a dinga tsokalanta.