IN KASHE MAZA ABIN YI NE…

0
1 views

DWi HAUSA – Waqa (Poetry) na Abusiddeeq A. AhmaduImage result for wife kill husband in nigeria

Idan kashe maza abin yi ne

Ya ku mata, ku je ku yi tata yi
Shege ka fasa dan halak sai yanka.

Guda nawa za ku kashe
Guda nawa za ku bari?
Ina basira ga mai rusa mafakarsa?

Ku ke daukanmu, ku na so ba kwa so
In ku ka ga dama, ku haifar a dadi
In ku ka qi, ku kifar a juji.

Kun ce mace mutum
Tabbas wannan gaskiya ne
Don in ba mace, waye mutum?

Related imageAmma fa wajen kashe mutum
A 6oye ko a sarari, a baki ko a zumd’e
Ai ba yanzu ku ka fara ba.

Don kuwa d’an mutum
Nawa ku ka haifa, ku ka haifar
Dubu nawa ku ka shayar, ku ka kayar?

Ga shi ku ne gatan yara
Sai dai kun fi kowa kashe su
Sannan dan tayi nawa, sai dai labari

Ga duka, ga zagi, ga karaya
Wasu ku zaune, wasu ku shaqe
Wasu ku gubar, har da masu yanka.

Kun fi kowa, kun fi komai son mutum
A wani jiqon, babu mai qinsa irin ku
Wata uwa ce don ta haifa, wata kuwa ko ba ta haifa ba.

Kun lahanta na ku, balle maraya
Matsalarku ba ta bar ku ba balle ta barmu
Kowacce kan ta ta sani, ba ku son junanku.

Image result for wife kill husband in nigeriaDuk inda ka ga mace na kuka
Tabbas da taimakon wata aka sa ta
Babu maqiyin mace kamar ita kanta macen

In jifa ya wuce kan ku, toh ya fada kan uban kowa
In ka ga mace na kushe abu
Toh ba kasonta a ciki.

Kun ce “Kishi kumallon mata”
Amma fa ku sani “Kishi ai ba hauka ba ne!”
Da za ku zam da shi mafakar kashe miji ko abokiyar zama.

Wata ta da6a ma sa wuqa ya na sallah
Wasu kuwa da tafasashe ruwa ko mai ku ka aika su
Wani layya ta yi da na ta, wata da guba ta kar shi.

Anya mata makasa mazan sunnah suna sallah kuwa?
Don Allah Ya ce sallah na hana alfasha da almunkari
In ka ga sa6anin haka, toh mutum ya binciki kansa.

Related imageAbu ne da mu ke jinsa daga nesa nesa
Yanzu wato nesa ta zo kusa
Abin qi, abin gudu yanzu mun ara ya zama na ado.

Shin ko kun san abinda wannan zai haifar
Rashin yarda da amincewa mata don zaman aure
Daga bisani haramun ya nemi zama halali, kaico!

Ya ku maza ku sani game da wasu matan
wAllaahi “Iska na wahal da mai kayan kara” ne
A yi dai mu gani, wata rana ba za a yi ba.

c.2018 Abusadeeq Ahmadu

6 total views, 1 views today

Comments

comments