DWi-HAUSA

GABATAR DA DesignWorld INTERNATIONAL-Hausa

Image result for Hausa

Jama’a assalam alaikum. Barkanmu da warhaka, kuma sannunku da jimurin hulda da mu a koda yaushe.Image result for Hausa

Sanadiyar neman da wasu da yawa daga cikin ma su sha’awar karanta abubuwan da mu ke kawowa mutane a dandalinmu na yanargizo wato intanet don mu sanar, fahimtar, wayar, ilimantar, fagar da kuma nishadantar da al’ummar duniya baki daya cikin harshe Turanci ta hanyar wallafa rubuce-rubuce a mujallarmu mai farin jini wato DesignWorld INTERNATIONAL (DWi), akwai ma’abota karatun harshen Hausa da su ka buqaci mu samar da wani bangare na wannan kafar sadarwa don a isar da wannan ‘karuwa ga dunbin al’ummar Hausawa da ma wadanda su ke amfani da harshen malam Bahaushe wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum a ko’ina a fadin duniya.

Image result for HausaToh, bacin hukumar gudanar da aiyukan tace rubuce-rubuce, labarai da rahotannin da dai makamantansu na wannan mujalla ta yi nazari kuma ta ga yiwuwar samar da wannan sashe a dandalin namu a yanar gizo, an yanke hukunci cewa a tabbatarwa da kasancewar wannan al’amari na samar da sashen Hausa na DesignWorld INTERNATIONAL. Za kuwa a dinga kiran wannan shafi da suna DesignWorld INTERNATIONAL-Hausa ko DWi-Hausa a taqaice.

Don haka duk wanda ya ke da sha’awar karanta dukkan abinda ya ga mun wallafa cikin harshen Turanci a dandalinmu na yanar-gizo wato website ke nan, toh, ya nemi kwatankwacin wannan rubutu a bangarenmu na DWi-Hausa, in sha Allaah zai samu. In kuwa bai samu ba toh, ya buqaci samun hakan ta hanyar rubuta mana wasiqa ya aiko akwatin email dinmu info@designworldinternational.com don mu duba yiwuwar samar da fassarar al’amarin cikin dan lokaci kankani.

Image result for HausaSannan kuma za mu yi amfani da wannan dama don mu aika da gayyata ga duk wani wanda ya ke da ta cewa dangane da dukkan wani al’amarin da ya shafi kasar da ya ke zaune ko shi a karankansa ko wasu, da ya rubuto mana abinda ya ji ko ya gani, ko ya bayyana ra’ayinsa ko ra’ayinta domin ma su tace rubuce-rubucenmu na cikin gida su duba yiwuwar wallafa shi/ita a shafinmu na DWi-Hausa. Albishirinku, don kuwa akwai da yawa ma su ilimin lamura daban-daban, masana, ma su yin sharhi dangane daa abubuwa da yawa na rayuwa da kuma al’adunmu duk sun soma aiko da rubuce-rubucensu don a buga ko muatane za su karanta su karu daga bayanansu.

Image result for HausaSannan kuma kofarmu a bude ta ke a koda yaushe don kar6ar gyara, korafi, kuskure in an samu, da kumar kar6ar dukkan wani abunda zai kyautata mana ayyukanmu don isar da sakonni yadda ya kamata a gareku. Za mu so kuma ma’abota karanta rubuce-rubucen da mu ka buga ashafukanmu na yanar gizo, cikin harshe Turanci da Hausa duk wanda ya ke da gudummawar da zai iya bayarwa ta fannin rubutu, wanda zai amfani al’ummar duniya, Najeriya, musammamma Hausawa a duk inda su ke a doron kasar nan da ya tuntu6i daya daga cikin editocinmu ta wadannan akwatinan email wato mmtijjani@designworldinternational.com, mmtijjani@gmail.com ko kuma mmtijjani@yahoo.co.uk.

Image result for HausaGa ma su hulda da dandalolin sada zumunta kuwa za su iya bibiyarmu a Fesbuk (Facebook) ta Facebook.com/DWinternational, a safinmu na Tuwita (Twitter) kuma a lalubemu a @DesignWorldINTL . Baya da wannan kuma akwai shafinmu a dandali baje kolin hotunan nan da ake kira Instagram domin kawo mu ku hotunan bukukuwan da aka gayyacemu na gangamin siyasa, taron ilimantarwa, daurin aure, buki ko suna da dai sauransu. Sannan kuma duk wani wanda ya ke da sanarwa, tallace-tallace, cigiya da ire-irensu zai iya tuntu6armu domin aiwatar ma sa da wannan bukatu cikin farashi daidai aljihunsa.

Image result for Hausa

Kar a manta, da zarar an hau dandalinmu wato www.designworldinternational.com toh mutum ya duba saman shafin daga tsakiya zuwa gefen hagu za ku ga an rubuta DWi-HAUSA, sai ku latsa wannan botir nan ta ke za’a kaiku shafinmu na rubutun Hausa.

Sai mun ji daga gareku. Kafin nan ga dan soma ta6i…

MATSALAR ALMAJIRCI