DALILIN SAKE-SAKEN AUREN MALAM BAHAUSHE (2)

0
107 views

…wanda ya rubuta Tijjani Muhammad Musa

DALILIN SAKE-SAKEN AUREN MALAM BAHAUSHE (2)
SanKano da Matansa

Toh, bari in dan maida mu baya kadan, kun san na ce mu ku son saduwa da mata da yawa wani al’amari ne da namiji a jinsin BaniAdama ya ke tattare da shi. Sanin wannan yanayi da Allaah SWT Ya yi wa d’an Adam ya sa Allah SWT Ya ba wa mutum damar ya auri mata ba 2 ba, ba 3 ba, har 4 idan zai iya daidaita tsakaninsu, in kuwa ba zai iya ba toh, ya auri daya wato dama ce ga mazaje Musulmi kawai.

Tunda Bahaushen mutum, musamman Musulmi mai tsoron gamonsa da Allaah ne ranar tashin alqiyama ya na iya qoqarinsa na ganin cewa bai sa6awa Allah ba. Inda in ya yi aure, ya kan kame kansa daga barin tsalle-tsalle, wato neman mata barkatai. Sannan da shike shi ba mutum ne mai yawan neman duniya ba, ban da cewa shi ba mai son neman duniya ta kowane hali ba ne, wato ya ki halak, ya ki haram sai ka same shi ba mai wadatar da zai dinga yiwa matan banza hidima ba ne don ya nemi biyan wata buqata ta sa daga garesu ba.

DALILIN SAKE-SAKEN AUREN MALAM BAHAUSHE (2)
Dr. Nura Ibrahim

Wannan dalili ya sa ala kulli halin matar nan ta sa kwaya daya tilo duk jarabarsa akanta ya kan qare. Ba shi da wani sukunin saduwa da wata daban in har ba halaliyarsa ba ce ta sigar aure. Sai dai fa kar mu manta akwai wannan bukata da ke tattare da kirarsa daga Ubangijin shi Allaah na cewa shima kamar sauran mazaje ya na da buqatar kwanciya da mace fiye da guda daya. Tunda kuwa ba zai iya riqe mata 2, 3 ko 4 ba don rashin wadata kamar yadda addininsa ya amince ma sa, ta yaya zai yi ya dinga biyawa kansa wannan buqatar da ke tattare da shi alhali ba zina zai dinga yi ba?

Hanya daya rak da ta ke bud’e a gareshi da ba zai sa6awa ubangijinsa ba, ba zai haifi dan shege ba, kuma shima zai samu damar saduwa da mata da dama kamar yadda sauran jinsi maza na bilAdama kan yi a sauran yarurruka, kasashe, nahiya daban-daban na duniya shine YA AURI MACE, YA SADU DA ITA. BAYAN WANI DAN LOKACI, YA SAKE TA A BISA WANI DALILI, DAGA BISANI YA SAKE AURO WATA. Nan ma bayan ya biya buqatarsa ta saduwa da ita, ya sake ta ya sake auro wata. Da haka da haka sai shima ya samu damar saduwa da mata da yawa ba tare da ya zalunci kansa ba. Tunda dai a cikin sigar aure saduwarsa da matan nan kan kasance.

Su kuwa wasu qabilu musamman wadanda ba Musulmi ba, saduwa da mata barkatai duk inda dama ta samu kama daga kan yammata, zuwa zawarawa, har ta kai kan matan aure, kai harma da maza ko mata tsakaninsu wato luwadi ko mad’igo ba wani abin kyama ba ne. Kun ga su wannan buqatar da ke tattare da yanayin halittar d’a namiji wato na son saduwa da mata da yawa babu hanin da su kan yi wa kansu dangane da wannan kazantar. Kusan su a wajen masu yi wannan ba kazanta ba ce ko kadan.

DALILIN SAKE-SAKEN AUREN MALAM BAHAUSHE (2)
Dhrarmendra da Hema Malini, daya daga cikin matansa biyu

Shi ya sa za ka ga a rayuwar wasu qabilun, wai don namiji magidanci ya na yin zinace-zinace, toh fa ba wani dalili ne na a zo a gani ba, ko na tada jijiyar wuya , ko na neman a zo ace za’a yi ma sa Allah wadai ba. A’a kusan ma abin ya zama abin kwalliya a gare shi. Ku san ma in ba shi da farka a waje, wato matarsa ce kawai ta ke sanin tsiraicinsa, toh fa shi da sauransa a zama gawurtaccen namiji.

Sannan kuma su ma matansu, tunda mazajen su na da matan da su ke nema a waje, sai su ma su ka daina killacewa mazajensu kansu. Da zarar mace ta samu wani wanda ta ga ya yi mata, ko ya tsananta nema a gareta, sai kawai ta ba shi damar ya biya buqatarsa akanta. In mijin ya nemi ya tada hankali, sai ta yi ma sa nuni da cewa ai shi ma yana yi da matan wasu, don haka dole ne shi ma ya haqura ayi da ta sa matar. In kuwa ba haka ba ne to ya daina. A wasu kasashen har ta kasance don miji ya kama matarsa da yin zina da wani, toh wannan ba zai zama hujjar da kotu za ta raba aure tsakaninsu ba. Turqashi!

Amma shi kuwa Bahaushe addininsa bai yardar ma sa da yin irin wannan rayuwa ba. Shari’ar Musulunci cewa ta yi in Musulmi ya kama matarsa da laifin zina, kuma ya tabbatar da haka toh zancen ya ci gaba da zama da ita bai taso. Domin ya tsaftace zuriyarsa kar a kawo

DALILIN SAKE-SAKEN AUREN MALAM BAHAUSHE (2)
Bahaushe

masa dan shege cikin ahlinsa, ya gaggauta rabuwa da ita ta hanyar sakinta wato ya raba auren da ke tsakaninsu. Ta hakan sai ta je ta ci gaba da abinda ta ke yi da wanda ta ke so ba tare da jawowa mijin na ta wannan kwamacala ba.

Kun ga tun da na ce mu ku Bahaushen mutum ba ya son yin zinace-zinace don tsoron in ya mutu ya za ta kasance tsakaninsa da Mahaliccinsa, toh shi fa kwanciya da mata barkatai ba na shi ba ne. Amma in har ya matsu da bukatar yin hakan toh auren mace 1, 2, 3, 4 shi ne mafita. Kuma ba zai yarda matarsa ta dinga zuwa wajen wani kwarto ya na saduwa da ita ba. Hakazalika ba zai lamunci wani kato ya dinga zuwa masa gida ya na satar kwanciya da ahalinsa ba. Muddin kuwa ya san hakan na faruwa toh, ba zai yi jinkirin sakin wannan mata ba, kuma ko wanene zai ce abin bai yi masa ba.

Su kuwa wasu qabilun su na sane da cewa matansu na da manema, kamar yadda su ke neman wasu matan a wajen gidajensu, amma kowa zai kau da kansa a ci gaba da rayuwa a hakan ana qirga shekaru da dama wai a sigar ana zaman aure. Sai ka ji namiji ya na ikararin cewa su yarensu ba su sakin matansu kamar yadda Hausawa ke yi. Ko ka ji mace ta na alfaharin cewa shekarunta 30 k0 40 da mijinta kwaya daya tilo ba su rabu ba kuma bai qara aure ba, amma da Bahaushe ne da yanzu ka ji ance aure ya mutu ko ya na maganar qara mata kishiya. Alhali kuwa daga shi har ita babu wanda ba shi da wasu mataye ko mazaje da su ke saduwa da su a wajen auren na su.

DALILIN SAKE-SAKEN AUREN MALAM BAHAUSHE (2)
Magidanci da matansa 3

Shi kuwa Bahaushe harka ce ta daga ni sai ke. In kuwa ya samu labarin cewa ke fasiqar mace ce, to gudun a kawo masa dan da ba na sa ba gida, sannan addininsa bai yardar ma sa da zama da wata mai kwarto ba, toh fa dole ya sallameta ko da kuwa ya na son ta. Shi kuma da ya dinga zaluntarta ya na sa6awa ubangijinsa toh ana so ba’a so sai ya nemi qara aure abinsa ya shiga saduwa ta halal. Sannan duk yaran da za a haifa ma sa e ya yarda su zama na halal komai yawansu kuwa.

Toh, kun ji dalilin da kan sa Hausawa yawan sakin aure ko kuma su ke da sha’awar qara aure maimakon zama da mace daya tilo.

(c)2017 DesignWorld INT’L/SWS.Comms

A Kiyaye Dukkan haqqin Mallaka

https://web.facebook.com/DWinternational/

222 total views, 1 views today

Comments

comments