DALILIN SAKE-SAKEN AUREN MALAM BAHAUSHE (1)

0
116 views

…Wanda ya rubuta – Tijjani Muhammad Musa

DALILIN SAKE-SAKEN AUREN MALAM BAHAUSHE
Bahaushiya

Malam Bahaushe dai yanzu ya yi qaurin suna wajen sakin mata idan ya auresu. In da har idan ya so wata mace qabilar da ba ta sa ba, ya bita garinsu wajen iyayenta don ya hada jinsi da su, shaidar farko da ake soma yi ma sa na dalilin rashin shakka ko qin aura ma sa wannan ‘ya ta su shi ne ba shi jumurin riqe mace na tsawon lokaci.

Wato ba shi da haquri jurewa mata matsalolin da ke tattare da halayyar su na zaman yau da kullum. Don da zarar mace ta ba shi haushi, toh fa babu tabbas cewa zai bari ta kwana a gidansa a wannan rana. Yanzu ne zai nuna mata hanyar gidansu ko ma hany
ar garinsu ya ce da ita waje rod.

Abin ya yi tsananin gaske da kusan wani bayanin da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta bayar na nuna cewa duk duniya babu wani jinsi da ya kai malam Bahaushe sakin mata. Gaskiya ko akasin hakan game da al’amarin abu ne da ke buqatar a fadada bincike kan wannan hasashe.

Amma kuma al’amari ne da kusan kowa ya shedi cewa Bahaushen mutum haqurinsa a koda yaushe dan gujub ne dangane da lamarin mata a harkar auratayya, wato a iya wuya ya ke ta fannin zamantakewa da matan da ya aura. Walau guda daya ce ko mai mata biyu (2) ne, uku (3) ko hudu (4) kamar yadda addininsa ya yarje ma sa.

Akwai da yawa da su ke mamakin hakan, kuma wannan al’amari ya kan daure mu su kai yadda wanda ake ganin ya fi kusan kowa tsarkake zaman aure, amma shine kuma ake ganinsa da yin abinda ya fi komai ban haushi a wajen ubangijinsa Allah Subhanahu Wa Ta’alah wato sake-saken aure.

DALILIN SAKE-SAKEN AUREN MALAM BAHAUSHE (1)
Hausawa

A kokarin gano me ke haddasa wannan mummunar sheda da aka yi wa malam Bahaushe mai ban haushi, na Tanko mai kan bashi,  binciken mujallar DWi Hausa ya kaimu wajen wani malami a  Jami’ar Bayero da ke birnin Kano mai suna Dr. Nura Ibrahim na tsangayar koyar da aikin jaridu wato Mass Communication Department inda ya fede mana biri har wutsiya, ya ganar da mu muhimmin dalilin da ya sa Bahushen ya ke da wannan “matsala”.

Da farko dai ya ce wannan al’amari ne da duniya sun taru wajen yi masa mummunar fahimta. Kuma da yawa ba’a kallon matsalar daga mahangar da ke nuna ainahin tushen wannan hali na malam Bahaushe. Sai dai kawai ma fi yawanci a kama kushe shi ba tare da yin duba da irin tsarin rayuwarsa ba.

Wannan tsarin rayuwa ta Bahaushen na da kwakkwarar alaqa da addinin da ya za6awa kansa wato addinin Musulunci. Sannan duk wanda zai soki malam Bahaushe dangane da yawan sakin mata in ya aura, toh ba ya duba da yanayin rayuwar Bahaushe da kuma rayuwar wani jinsin daban don ya fahimci banbancin da ke akwai tsakanin biyun.

Daga bisani sai ya ce rashin yin hakan kuwa ba qaramin rashin adalci ake yi wa malam Bahaushe ba wajen kushe shi dangane da irin riqon da ya ke yiwa wannan sunnah ta Annabinsa, a ra’ayin wasu. Amma kuma in an duba da kyau akwai wani boyayyen sirri tattare da al’amari wanda fahimtar haka ka iya kawowa Hausawa samun mafita.

DALILIN SAKE-SAKEN AUREN MALAM BAHAUSHE (1)
Dr. Nura Ibrahim

Don a mahangar wannan malamin tsagayar akwai zalunci wajen daukar wannan matsaya, alhali kuwa addinin da mutum ya ke bi in dai da gaske ya ke yi, toh, ya kamata ace yana da tasiri a wajen aiwatar da lamuransa na yau da kullum. Daga nan sai malamin ya kawo bayanin dalilin da ya sa wannan hali ya kasance da Bahaushe.

Toh, ga abinda wannan malami ya kawo, ku taya ni dubawa.

Da farko cewa ya yi kowa ya san malam Bahaushe idan ya yi aure, toh, in ba fasiqi ne shi, mai wasa da addininsa, maras tsoron Allah toh da wahala ka same shi ya na neman matan banza a waje. Sau da yawa ya kan ke6e kansa dangane da buqatunsa na saduwa da mace ga matarsa ta sunnah kawai.

Sa6anin wasu yaruka wadanda za ka ga cewa duk da sun yi auren, ba kasafai su ke kame kansu daga barin neman mata a waje ba. Kuma wannan nema da su kan yi ba don qara aure su ke yinsa ba sai don kawai biyan buqatarsu ta saduwa wato yin zina ke nan. Da zarar sun kwanta da wacca su ka nema sai su raba hanya da ita su nemi wata, nan ma a kuma.

In an lura da kyau wannan wani hali ne da duk duniya d’a namiji daga kowace nahiya da kuma kowane jinci ya kan yi, sai dai abinda ba’a rasa ba. Wato maza su na da sha’awar su sadu da mata fiye da guda daya a ko da yaushe. Duk inda dama ta samu namiji kan so ya samu mata ace yana saduwa da su. Yau ya kwanta da wannan gobe ya kwanta da waccan. Kuma zai yi duk iya qoqarinsa domin ya tabbatar ya samu hakan ta kasance.

DALILIN SAKE-SAKEN AUREN MALAM BAHAUSHE (1)
Bahaushe

Toh, a duk jinsin yarukan duniya Bahaushe ya na daga cikin wadanda su ke gudanar da rayuwarsu akan tafarkin addinin Musulunci. Don kusan Bahaushe ya fifita ala’dar Musulunci akan ta sa al’adar ta gargajiya. Duk inda aka ce ya na da wani al’amari da ake gudanarwa a gargajiyance, in dai har aka ce ga yadda addininsa ya ce ya yi, toh ya kan ajiye al’adar nan ta gargajiya ya bawa Qur’ani ko hadisin Mazonsa fifiko akan lamarin.

A dalilin haka ya sa in Bahaushe ya yi aure, ya kan tattara dukkan sha’awarsa ya maidata kan matarsa da ya aura wato ya kan yi iya qoqarinsa ya guji yin zina da wata matar da ba ta sa ba. Kun san babu abin kunya a wajen dukkan wani sahihin Bahaushe fiye da ace yau ga shi an kama shi da wata mace suna zina ko a kawo masa d’a daga waje a ce na sa ne, kuma ta kasance daga hanyar zina aka sama ma sa wannan zuriya.

Amma kuma da yawa ana sane da cewa wasu yarukan, riqon addinin Musuluncinsu sau da yawa ba za ka ga sun dauke shi da muhimmanci ba. Kusan ma a suna abin ya qare. Don haka wai ace su ji tsoron Allah su guji neman matan banza a waje duk da shike su na da aure bai ma taso ba. Kusan ma abin alfahari ne a wajen wasu a ce suna da farka a waje, kuma ba daya ba ba biyu ba da su ke mu’amala da su ta kowacce siga kuwa.

Akwai ci gaba a kashi na biyu (2)

(c)2017 DesignWorld INT’L/SWS.Comms

A Kiyaye Dukkan Haqqin Mallaka

https://web.facebook.com/DWinternational/

217 total views, 1 views today

Comments

comments