ZANTA-ZANCE DA MAIMUNA BELI

0
114
Zanta-Zance Da Maimuna Beli
Maimuna Beli, Tauraruwar BBC Hausa HIKAYATA 2017

DWi HAUSA

Related image

SARAUNIYAR HIKAYATA 2017 TA BBC HAUSA

Maimuna Idris Sani Beli fitacciyar marubuciya kuma mawallafiyar litattafan Hausa ce ta lashe gasar rubuta qagaggen Labari wato HIKAYATA 2017 da BBC Hausa ta qirqiro don inganta harshe, ha66aka adabi da kuma ba mata damar nuna basirarsu a harshen Hausa wacca  su ka faro a shekarar da ta wuce.

Tambayar da mu ka yi kwanaki na cewa shin wai wacece Maimuna Beli ne? Wato marubuciyar da ta cinye gasar da labarinta mai taken BAI KAI ZUCI BA. Yanzu haka dai amsar wannan tambaya da ma wasu sun bayyana ta hanyar wata hira ta musamman da tauraruwar ta yi da mujallarmu DesignWorld INTERNATIONAL (DWi).

A zaman da ta yi da daya daga cikin ma’aikatanmu Tijjani Muhammad Musa inda su ka zanta-zance wacce mu kan yi da shahararrun mutane maza da mata da su ka cimma wani buri a rayuwarsu wato TEE TALK a Turance, wannan gwarzuwar marubuta adabi ta warware mana zare da abawa, inda ta yi bayani akan abubuwa daban-daban da su ka shafi rayuwarta da kuma harka rubutunta.

Yanzu haka dai saura ‘yan kwanaki kadan a yi bikin karrama matan da su ka sami cin nasarar lashe wannan gasar a wani biki na musammam da BBC Hausa ta shirya wanda za’a gudanar a babban d’akin taro na Ladi Kwalli na katafaren ‘otal din nan da ke Abuja wato Sheraton Hotel & Towers ranar Juma’a 24 ga watan Nuwamba, 2017.

Sai dai kamar yadda mu ka yi wa mabiya da makaranta mujallarmu ta DWi alqawarin kawo mu ku wannan hirar da tauraruwar marubuta gasar Hikayata ta BBC Hausa, toh “Kyaun alkawari, cikawa.”

Sannan ku sani in ba anan ba, babu inda za ku je ku karanta wannan ke6a66iyar hirar da wannan baiwar Allaah a karon farko idan ba shafukan mujallarmu ta DesignWorld INTERNATIONAL (DWi) ba.

Image may contain: 1 person, smiling, closeup

Yanzu sai ku shirya tsaf don jin me Maimuna Idris Sani Beli za ta ce kafin mu kawo mu ku yadda bikin karramata da sauran mata marubuta adibin Hausa zai kasance a birnin tarayya Abuja.

***

DWi:  Bari mu fara da taqaitaccen tarihin Maimuna Idris Sani Beli. Ko wacece ita?

Maimuna Beli: Sunana Maimuna Idris Sani Beli. An haife ni a shekarar 1983 a Unguwar Galadanci ta cikin birnin Kano. Na yi Jarqasa Primary school, sannan na tafi GGSS Qwa na fara Junior secondary, ban kai ga kammalawa ba aka cire ni aka yi min aure. Daga bisani na koma makaranta na kammala sakandare sannan na yi National Diploma a 6angare computer tare da wasu kwasakwasai. Na yi koyarwa ta wasu shekaru. Ina da aure da ‘ya’ya biyu.

DWi:  Yaushe ki ka fara rubuce-rubuce?

Maimuna Beli: Na fara rubutu ne a shekarar 2003

DWi:  Waye ko wacece ta gano kina da basirar iya rubuce-rubuce?

Maimuna Beli: Eh, to. Ai kuwa dai kafin na fara rubutu kowa a zallar Maimuna ya ke kallona, ba a jona komai a bayan sunan ko gabansa.

DWi:  A ina ki ka koyi yadda ake rubutu ko mu ce wa ya koya mi ki?

Maimuna Beli: Farko na koyi rubuce-rubuce ta hanyar litattafan da na ke karantawa saboda asali ni makaranciya ce. Saboda haka lokacin da zan fara rubutu ma wad’annan litattafai na zube su ka riqa raka ni. Sai daga bisani da na gane wautata cewa ba su isa ba. Sannan na fara neman masana da kuma marubuta.

DWi:  Da wane rubutun ki ka fara? Shin ko ki na da shi a ajiye?

Image result for bbc hausa hikayata 2017

Maimuna Beli: Na fara da littafina ‘Tun daga tushe’. Ba ni da rubutaccensa, amma ina da bugaggensa.

DWi:  Ko menene ya ke motsa mi ki tunani har ki ji kina son ko sha’awar ki fara rubutu? 

Maimuna Beli: Wata malama ke wa’azi, na ji tana sukar cewa litattafan Hausa na lalata tarbiya saboda sakin baki a ciki. Sai na ji cewa ai za a iya rubutu, saqon ya isa ba tare da sakin bakin ba. Don haka na yanke shawarar gwadawa.

DWi:  Akan me ki ke yi son ki yi rubutu a mafi akasarin lokaci? 

Maimuna Beli: Duk abinda ya ratsa tunanina da idona da kunnena. Kai wani lokacin har da mafarkaina. In dai abin ya ta6a raina, sai in ji ina son rubutu a kai, ko da kuwa a iyakar son yin zan tsaya, ma’ana ba zan samu dama ba.

DWi:  Yaya ki ke ganin tasirin rubuce-rubuce wajen fargar da al’uma akan komai na rayuwa? 

Maimuna Beli: Alqalami ai mai canja duniya ne, ba ma al’ummar cikinta ba.

DWi:  Shin wannan al’amari na isar da saqo ta hanyar yin rubutu ko malam Bahaushe ya dauke shi da muhimmanci kuwa? 

Maimuna Beli: Eh to! Da sauqi gaskiya. Don muna da kasalar son karatu. Sannan ga yi wa abu hukunci in ya zo a matsayin sabo. Sai ya zamana duk hukuncin da aka za6a masa har ya gama tsufansa sai an sami masu tafiya akan wannan hukuncin, daidai ne ko ba daidai ba ne. Farkon irin litattafanmu ai sun fuskanci qalubale, aka dinga gudun litattafan da marubutan. To har yanzu akwai 6ur6ushin wannan hukuncin, inda wanda bai san me ke qunshe cikin littafi ba ma zai iya tsinewa littafin, bare har ya yarda ya karanta ko wani nasa ya karanta ya sami saqon da ke ciki. Amma dai ana samun cigaba ba kad’an ba. Don da wahala ka yi rubutu ba ka sami wanda zai kira ya ce maka ya qaru da abinda ke ciki ba.

DWi:  Adabi wata hanya ce da al’uma ko jinsi kan yi amfani da shi wajen ajiye tarihinta, bayani akan al’adunta, koyar da dabi’unta, ilimantarwa, wayarwa, koyarwa da dai makamantansu. Shin hakan na samuwa a wajenmu kuwa?

Image may contain: 1 person, closeup

Maimuna Beli: To ana kwatantawa, amma akwai fargabar idan hakan zai d’ore. Musamman da na yi maganar kasalar karatu da muke da ita. In masu taskance tarihi da al’adun da komai ma ba su biye wa masu qin nuna sha’awa ga ayyukansu ba, qila ba za mu koma a gaba idan muna son jin tarihinmu na baya ko wani abu da ya dangance mu sai dai mu kunna wayarmu ta hannu ko mu kunna talabijin ba, don a yanzu radio ma an fara juya mata baya.

DWi:  In kuwa ya na samuwa, ki na ganin abinda ake yi ta wannan fannin ya wadatar kuwa? 

Maimuna Beli: Bai wadatar ba, ana dai kwatantawa.

DWi:  Ina kuma kira da ake yi na a soma koyar da yaranmu a dukkan makatantunmu daga Nazareth har zuwa jimi’a a cikin harshen uwa kamar yadda sauran kasashe da jinsin da su ka ci gaba a duniya ke yi? Me za ki ce akan wannan? 

Maimuna Beli: Ni kam ina maraba da wannan quduri wAllahi. Don duk qasar da ke koyarwa da yarenta ba ma za ka had’a kafad’arta da wadda ke jidalin koyar da ilmi da yaren wasu, sannan su zama su na koyan baqon yaren a lokaci guda ba. India na koyarwa da yarenta, kalli likitocin da su ke haifa. China ma haka, kalli qere-qere da su ke ta samarwa.

DWi:  Maimuna Beli ta yi fice ne a fagen rubuce-rubuce cikin harshen Hausa, da wane rubutunki wannan fasa-taron ya soma samuwa, kuma yaushe?

Maimuna Beli: Anya ni zan iya tabbatarwa kuwa? Ka san yadda mutane su ka bambanta akan abubuwan da ke mu su dad’i. Duk kashin abinda ka rubuta sai ka sami wanda ya yi masa dad’i. Saboda haka na wayi gari ina rubutu kullum kuma ina qara samun ma su zuga ni da cewa na rubuta mu su daidai. Yaushe ne hakan ta faru? Tunda a hankali ne ba, zan iya tabbatarwa ba.

DWi:  Wace hanya ki ka bi har aka soma yi mi ki shaidar ki na da baiwar iya rubutu? 

Image result for bbc hausa hikayata 2017

Maimuna Beli: Ina bibiyar malaman ilmi da na falsafa. Na koyi azancin magana daga nasu azancin cikin horewar ubangiji. ‘Daya kenan daga cikin abinda ke d’aukar hankalin makarantana.

DWi:  Ga dukkan marubuci mace ko namiji akwai qalubale bila-adadin da kan kawo mu su tarnaqi da cikas wajen samun kar6uwa ga jama’a, da wanne ki ka fara? 

Maimuna Beli: Tsakani da Allah ina daga cikin mutanen da in wuya ta wuce ba ma na tuna ta a matsayin wuyar, ko da zan fad’a sai in ga kamar cancanawa da zugugu ne.

DWi:  Wannene daga cikin karya-lagon da aka yi mi ki ya fi sauran ta6a ki har ki ka ji kamarma ki daina yin rubutu gaba daya a rayuwa?

Maimuna Beli: Ban ta6a jin cewa in daina rubutu ba. Rubutu na da shiga rai. Duk marubuci zai fad’a ma ka rubutu ya fi taba kama maqogwaro. Wuya ba za ta sa a yi fushi da shi ba. Sai dai dalilan da su ka faskari rayuwa su hana marubuci rubutu. Kuma dole za su bar shi da begensa.

DWi:  Kafafen sadarwa musamman Jaridu da Mujallu na da gagarumin gudummawar da ya kamata su dinga bayarwa wajen zaqulo marubuta har duniya ta san su. Shin a rayuwarki ta wannan sigar ko kin samu irin wannan dama kuwa?

Maimuna Beli: Na samu ta hanyar gasar da kafar yad’a labarai ta BBC ta sanya a halin yanzu.

DWi:  Rubuce-rubucenki ta ina su ka fi fita su isa ga al’umar gari? Shin ta jaridu ne ko ta litattafai? Me ya sa? 

Maimuna Beli: Ta hanyar litattafan da nake wallafawa dai. Radiyo da jaridu duk sun san ni ne ma ta dalilin wallafe wallafena.

DWi:  Kawo yanzu litattafai nawa ki ka wallafa, kuma wannene na farko? Wanne ki ka fito so? Wane littafinki ne Bakandamiyarki?

Maimuna Beli: Na wallafa litattafai goma sha biyu (12), ‘Tun daga tushe’ ne farko. Ina alfahari da ‘Goran duma‘ amma bakandamiyata ‘Gwanin Na iya…’

DWi:  Buga littafin marubuci na farko na tattare da rashin-sani, rudani, quntata da makamantansu. Ta yaya ki ka shawo kan irin wadannan tashin-tashina?

Maimuna Beli: Sai gashi ni ban fuskanci wannan quntata da tashin-tashinar ba kuma wAllahi. Kamfanin da ya yi min wallafa ya yi iyakar nasa qoqarin.

DWi:  Ko kin maida kudin da ki ka kashe wajen buga littafinki na farko kuwa? Ki na samun tallafi daga wani wajen nema don buga litattafanki? 

Maimuna Beli: Ai ba a 6ari a kwashe duka. Kud’in kam ta ina za su dawo duka? Ai sun tafi a dunqule ne su ka dawo a warware. Wani ma bawa na aika garinsu. Tallafi kuma ana samun na addu’a da qarfafa gwiwa, na kud’i ne dai tukunna.

DWi:  Wadanna saqonni ki ke kokarin isarwa ga Hausawa da ma duniya baki daya ta rubuce-rubucenki, musamman litattafanki? Shin su na isa kuwa?

Maimuna Beli: Saqonnin litattafai na isa sosai, tunda ta dalilinsu sai da na zama malamar gyaran aure da sauran al’amuran yau da kullum. Makaranta na d’ora nauyin warware matsalolinsu wa marubutansu, don haka marubuta kan qara tashi tsaye wajen neman ilmi ko dan sauke wannan nauyi, wanda ina ciki. Ka ga kuma duk tasiri litattafan ne. Marubuci ya warware matsalar tauraron littafi, sai tauraron gaske ya zo da tasa matsalar.

Image result for bbc hausa hikayata 2017

DWi:  Banda wannan nasara ta lashe gasar HIKAYATA 2017 ta BBC Hausa, wace gasar ki ka lallasa wasu kuma? Jero su mu ji,  in akwai. 

Maimuna Beli: Na ta6a shiga gasar rubutun gajerun labarai ta Makarantar Malam Bambad’iya shekarar 2013, amma ni aka lallasa. Don cikin mu talatin da bakwai (37) ne na ke jin na yi ko ta sha biyu (12) ko sha uku (13) ko ma ta sha hud’u (14), ina jin jina-jinar da aka yi min ce ta sa na manta.

DWi:  Ya ki ka ji da sakamakon fidda zakarar gasar BBC ya bayyana cewa Maimuna Beli ce ta cinye kyautar farko?

Maimuna Beli: Na ji abinda ban ta6a ji ba, don haka ba zan iya kwatance ba. Ba zato ba tsammani na shiga gasar duniya cikin gogaggun marubuta a ce na zo ta d’aya? Haba! Sai ka ce wata Antaruwa.

DWi:  Me za ki yi da kudin da za’a ba ki na kasancewa gwanar gasar BBC ta wannan shekara ta 2017?

Maimuna Beli: Toh fa! *murmushi* Wannan tambayar a rataye ta.

DWi:  Akwai zuwa Abuja bikin karrama ki da sauran matan da ku ka shiga wannan gasar don fafatawa tare. Me za ki ce in an kira ki kar6ar lambar yabonki?

Maimuna Beli: Zan tattara ‘yar basirar da ta rage min in bayyana murna ta bisa wannan dama da BBC su ka ba ni, inda su ka kawo ni kusa da burina. Wato aika saqonnina ta hanyar rubuce-rubuce, don maudu’in labarin da ya ci gasar ya dad’e ya na yi min quna a cikin raina. Sai ga dama ta samu wadda zan yad’a shi fiye da a ce a littafi na rubuta na fitar.

DWi:  Matasa mata nan gaba za su so kwaikwayonki tunda gashi BBC Hausa ta jinjina kwarewarki a game da rubuta qagaggen labari, wace shawara za ki ba su?

Image result for bbc hausa logo

Maimuna Beli: Qoqari shi ke bud’e qofar da ke bud’e. Abinda mai ta’alimi ya ce ke nan. Da qoqari ake samun d’aukaka, ba da Kaka ba. Mu dage mu yi aiki tuquru kuma da gaske. Duk abinda za mu rubuta mu yi da ilminsa, daga rubutun kansa har abinda za mu rubuta. Wannan ita ce shawarata ga masu tasowa irina.

DWi:  Shin ko akwai shirin koyawa na baya iya rubutu ta hanyar shirya bitoci?

Maimuna Beli: Dayake wuyana ba wani kauri ya yi ba, ni ma d’aliba ce me neman ilmi, koyo na ke har yanzu. Amma dai in an nemi shawarata game da rubutu ina bayar da iyakar qoqarina. Bita kuma sai dai na shiga rububin qungiyoyin da na ke da d’an qarfi a cikinsu na bayar da tawa gudunmowar.

DWi:  Mutane yanzu da dama ba su son yin karatu, kai ba yanzu ba ma tun a da, sai dai yanzu abin ya qazanta saboda zuwan hanyoyin sadarwa na zamani irinsu bidiyo da intanet wato yanar-gizo, ta yaya ki ke iya sa mutane karanta rubutunki? 

Maimuna Beli: Akwai wannan qalubalen tabbas. Amma kamar yadda na fad’a a baya, ka rubuta mai kyau. Mutum ko shi ne Russia ba ma wai abinda aka qera ba, sai ya nemo rubutunka ya karanta in dai mai sha’awar karatun ne.

DWi:  Yanzu dai zamani ya zo mana da wata sabuwar hanyar sadarwa inda kowa da kowa ba wai kawai sai fitattu a wasu harkokin rayuwa ba, zai iya bude dandali (website) ko shafi (social media pages) a yanar-gizo wato intanet ya baje kolin fasaharsa don duniya ta sani kuma dukkan mai buqatar ayi hulda don samun fahimta, ilimi, kudin shiga da dai sauransu zai iya tuntu6ar mutum daga ko ina a doron qasa. Ko Maimuna Beli na da ire-iren wadannan dandali ko shafuka a yanar-gizo kuwa? 

Image result for bbc hausa hikayata 2017Maimuna Beli: Ba ni da shi a halin yanzu, amma akwai niyya.

DWi:  Da yawa daga cikin marabutanmu a Arewa ko ma ince a Najeriya ba su rungumi sabon salon yada rubuce-rubucenmu ta intanet ba, balle su soma siyar da litattafensu ta kafofin da ke wannan dandali irinsu amazon.com da dai sauransu. Shin a matsayinki na tauraruwar rubutun Hausa ko kin fara hakan kuwa?

Maimuna Beli: Na fara gwaji da Okada Books, inda na d’ora litattafaina biyu. ‘Rigar Siliki’ da ‘Mafarkin Khadija’. In ta yi dad’i ragowar ma za su biyo baya.

DWi:  Daga karshe, mu na taya ki murnar lashe wannan muhimmiyar gasar ta mata zalla marubuta a cikin harshen Hausa ta BBC Hausa wato HIKAYATA 2017 da labarinki mai taken BAI KAI ZUCI BA. 

Maimuna Beli: Na gode

DWi:  Maimuna Idris Beli mu ne ma su godiya da ki ka samu damar yin wannan hirar ta musamman da Mujallar DesignWorld INTERNATIONAL – HAUSA (DWi). Sai mun sake gayyatarki nan gaba don hirar ta mu da ke, ba ta qare ba.

Allah Ya qara basira, Ya bada sa’a, Ya huce gajiya.

Maimuna Beli: Ni ma na gode, In sha Allah ana tare. Amin ya Rabbi.

***

~ Edita, DesignWorld INT’L – Hausa

https://web.facebook.com/DWinternational/

Comments

comments