WAYON ACI, WAI AN KORI KARE…

0
391

WAYON ACI, WAI AN KORI KARE DAGA GINDIN ‘DINYA

Aure dai kowa ya san sunnar Annabi Muhammadu sallahu alaihi wa salam (SAWS) ce. Kuma hadisai da yawa sun nuna cewa aure na daga cikin abubuwan da ake so dukkanin Musulmi, musamman maza ma su sukunin yinsa daga matasa har zuwa manya su yi shi.

Aure kuma ya kasance akwai ayoyin alQur’ani da kuma hadisan Manzon Allah da dama da su ke nuni da muhimmancinsa, sannan ta yadda za’a gudanar da shi, salo wato sharud’d’an yinsa, su wa da wa aka yarda su yi da dai makamantan wannan.

Babban dalilin yin aure kuwa ba komai ba ne illa ya hana Musulmi mazansu da matansu yin zina. Wanda samun haka ya kan haifar da al’umma sahihiya, mai nagarta, ingatacciya da dai sauransu. Baya da wannan, aure kan kare mutumcin mutum kuma ya kan sa a samu zuriyya dayyiba.

Wannan al’amari na samun abokiyar zama ga d’a namiji ya na daga cikin ni’imomin da Allah Subhanahu Wa Ta’alah Ya yassarewa dukkan jinsin bani Adama, inda babu wasu rukunin mutane da Allah Bai ba su damar samun wannan natsuwa ta hanyar jin dadin zama da mace ba.

Kusan kowa daga mai arziqi zuwa talaka, mai ilimi da jahili, mazauna birni da na ‘kauye, farare da baqaqen mutane, ma su hankali da ma mahaukata, da ma su bautawa Allah da ma su shirka kai harma da wadanda su ke ikirarin cewa babu Allaahnma baki daya, duk babu wanda Allah Ya haramta masa ni’imtuwa daga falalar ‘ya mace.

Sannan saboda irin sanin da Allah Ya yi dan Adam, sai Ya yarje d’a namiji da ya auri mata daya bayan daya har guda hudu. Su kuma mata Allah Ya umarcesu da auren namiji kwaya daya jallin jal. Babbar hikima anan itace don yaran da za su biyo bayan saduwa tsakanin ma’auratan biyu su san waye mahaifinsu. Sabanin ita uwa da ba za ta iya tantance uban ‘ya’yanta ba in har namiji fiye da daya su ka kasance ma su kwanciya da ita.

Banda wannan kuma bincike ya nuna cewa namiji a yanayin da Allaah SWT Ya yi shi halittarsa mai son saduwa da mata ne barkatai. Ita kuwa mace a yadda Allah Ya yi ta, mafi akasarinsu ba ma su son namiji fiye da daya ba ne ya san tsiraicinsu.

Don haka Allah cikin ikonSa Ya tsarawa namiji damar sanin ‘ya mace fiye da daya, wato Ya saukar da aya a cikin littafinSa mai tsarki wato al-Qur’ani cewa mutum dan Adam zai iya auren mata 2 ko 3 ko 4 in zai iya adalci tsakaninsu. In kuwa ba zai iya daidaita tsakaninsu ba toh, ya auri guda daya tilo.

Da wannan Musulmi su ke kafa hujjar auren mace fiye da daya, a inda za ka ga wasu har mata hudu rigis su kan aura su yi ta fantamawa da su in da sukuni, in kuwa babu su yi ta fama da su ba tare da suna ba su haqqoqin da shari’a ta tanadar aba su ba. Wasu na da kyawawan hujjoji na qara aure, amma wasu kuwa fariya ce da karambani kan sa su yin hakan.

Kadan daga cikin dalilan da su kan sa mazaje qara aure bacin sun yi ta farko sun hada da samun wadata ko daukaka, rashin fahimta, jituwa, zaman lafiya da dai sauransu tsakaninsu da matarsu ta farko. Akwai kuma rashin haihuwa, rashin lafiya, yin gasa tsakanin abokai, dadewa a wani gari da ire-iren wadannan.

Baya da wadannan dalilai akwai kuma yawan mata da su ka kai munzalin yin aure amma babu isassun mazajen da za su bugi kirji su ce “Cas” in an ce mu su “Kule!” Sai ka ga maza ma su aure sun fi matasa karfin zuciyar yin auren, tunda mafi yawancin marasa auren fari na tsoron daukar dawainiyar ‘ya mace.

Sannan talauci ya na daga cikin abinda kan sa ayi qarin aure. Ba fa ta bangaren magidanta ba, a’a ta wajen iyayen yara mata. Sau da yawa za ka ga saboda rashin wadatar samun ilimantar da ‘ya’yansu mata iyaye da yawa kan matsawa yarinya ta yi aure don a kawar da ita daga gaban iyayen tunda ta soma jinin al’ada a gidansu.

Wannan yanayin na balagar ‘ya mace a gidansu ya na tattare da hadarurruka ma su tarin yawa inda za ka ga hankalin iyaye na tashi saboda gudun kar ‘yar ta yi sakaci samari, marasa kyakkyawar tarbiya su hure mata kunne, su yaudareta a tafka abin kunya.

Yarinya in ta kai munzalin sanin da namiji, al’amari ne da ke tattare da hadarin gaske. Na daya dai mafi yawancin ‘yammata a wannan yanayin su na fama da wani irin juyin-juyahalin da kan sa su cikin rudani. Wasu sinadarai ne kan bijiro mu su ta bangarori dabandaban a jikinsu ma su sa su sha’awar da namiji.

A wannan yanayin da kan sa mata cikin garari, sau da yawa sai ka ga yarinya ta soma wasu halayyar da ita kanta ba ta san dalilan da ya sa ta ke yinsu ba balle ta fahimcesu. Kawai dai za ta ga maza da yawa sun soma yawan kallonta, su na yawan kula ta, su na janta da wasa, suna yawan tsokananta, ita kuma ta na jin dadin wadannan kulawa.

Kuma duk sanda aka ta6a ta, wato aka kama jikinta musammanma idan d’a namiji ne, toh sai ta ji wani nau’in dad’i a tattare da ita. Ba kasafai akan samu yarinya ta iya kama kanta ko ta hana kanta yarda ko son a dinga jan ta da ire-iren wadannan wasanni ba. Kusan ko da yaushe za’a ga tana bibiyan son hakan.

In kuwa aka samu rashin dace, aka samu rashin tarbiyya irin na addinin Musulunci da tsoron Allaah da koyarwa AnnabinSa, da zarar an samu ke6antaka, sai ka ga an kama aika-aika. In kuwa abin ya dore, toh cikin dan lokaci qanqani sai ka ga abin gudu, abin kunya ya faru, a sami yarinya da juna biyu wato cikin shege ke nan.

Don gudun kar hakan ta faru Manzon tsira Annabi Muhammad SAWS ya yi umarni da agaggauta aurar da yarinya in ta kai wannan ga6a na rayuwarta. Ba don komai ba sai don kar a barta cikin wannan al’amari wanda ya na da wuyan sha’ani da kamewa ga manya ma, balle kuma ace ga yarinya waccan ba ta san yadda ake shawo kan al’amarin ba.

Don haka iyaye ke Allah-Allah su samu wani wanda zai nemi auren ‘yarsu da zarar wannan yanayin ya zo wa yarinya. Kuma a yadda rayuwa ta ke wanda zai so ko ya qaunaci wannan yarinyar ba lallai ba ne ace auren fari zai yi ba. Wani a ta biyu ko ta uku kai har ma ta hudu zai iya cewa yana son ya aureta.

A wajen yarinyar muddun ta ji ta na sonsa toh fa an gama, don kuwa komai na iya faruwa, musamman in ba ta da kyakyawar tarbiyya. Don kuwa in ba’a gaggauta aurar da ita ba, tabbas sai ta nemi ta ba shi kanta a asirce. In kuma ba shi da tsoron Ubangijinsa, sai ka ga ya kama yin abubuwa da ita daga baya ya ce ya fasa aurenta.

In kuwa aka yi sa’a aka yi auren yadda addinin Musulunci ya shar’anta, toh sai ka ga dukkan fitintunun da ka iya biyowa baya an samu sauqinsu ko kuma sun kau. Bacin dan lokaci kankani sai ka ji yarinyan nan da ciki, wanda bayan wata tara sai ta zama uwa. Daga bisani ta zama kammalalliyar matar aure da yaranta.

Inama a hakan zancen ya kan qare. Amma ina fa! Rashin adalci, cin mutunci, zalunci, wulaqanci, zagi, cin zarafin iyaye, gori, tauye haqqi, takura, rashin ko in kula, kunci, tozarta, wallafa, tashin hankali da tashin-tashina, ta yau daban ta gobe daban daga wajen mijin zuwa ga matar sai ya zamo shine abin yi kulli yaumun.

Ita kuma matar butulci, rashin ladabi, rashin tsafta, kin bin umarni, gulmace-gulmace, shiga sharo ba shanu, ciyo bashi, tauye kudin cefane, almubazaranci, tonon asiri da na silili, rashin girmama iyayen miji, wasa da girki, sakaci da wulakanta dukiyar miji, wasa da ibada, kwantata miji da na wata, ja wa miji rai, yawan fice-fice, tara abokan banza, fifita na ta akan na sa da dai ire-iren wadannan sai su gurbata auren.

Toh fa kowa ya sani, mutumcin ‘ya mace a addinance da kuma a al’adance ya na tattare ne da rayuwarta a gidan mijinta ba a gaban iyayenta ba. Don da zarar mace ta kawo karfi babu abinda ta ke so illa ta samu cin gashin kanta, wato ya zam cewa ita ta ke juya kanta da kanta kuma ta yi abinda zuciyarta ta raya mata, sanda ta so, a inda ta so da wanda ta so ba tare da jin shakkar kowa ko komai ba.

Wanda samun yin hakan in ya gamu da tashen balaga, quruciya, ga6anci da dai iren-iren wadannan halaye na rashin hankali, ba ko da yaushe hakan kan haifar da d’a mai ido ba. A wannan ga6ar ne mafi akasarin yara matasa musammam mata su kan samu kansu cikin aikata kurakuren da kan sa su da-na-sanin da iya tsawon rayuwarsu ba zai ta6a gyaruwa ba.

Su kuwa iyaye, a wannan lokacin ne na kiwo ‘ya’yan su ke fuskantar mafi kololuwar qalubale, tashin hankali, tirjiya, fargaba da barazanar cewa dukkan wahalhalun da su ka sha na tsawon lokaci wajen kiwo da tarbiyar ‘ya’yansu maza ko mata zai tashi a aikin banza, in dai har su ka bari yaro ko yarinyar ta fandare mu su.

Don tabbatar da hakan bai faru ba hanyoyi biyu iyaye kan yi amfani da shi don samun mafita. Ga d’a namiji akan sama masa aikin yi wanda zai je shi can ya dinga yi yana samun abinda zai shagalatar da shi, ya gajiyar da shi ta wannan sigar kuma ya ga kudin shiga su na samuwa a gareshi. Ita kuwa mace, babu abinda ya kan sadudar da ita da ya fuce ayi mata aure.

Kuma a zamanin daa daga d’a namiji har zuwa ‘ya mace duk wanda ya ishi iyayensa da ma mutan gari da giggiwa da qin ji a kasar malam Bahaushe musamman a karkara, toh aure akan yi mu su, wanda cikin dan lokaci qanqani za ka duk sun yi ladab, jikinsu ya yi sanyi sun komo hayyacinsu musamman in su na so da kaunar junansu. Kafin kuwa ka ce wani abu, jikoki su kunno kai. Shikenan zancensu ya qare.

Ta hakan iyaye musamman ma su raunin wadata ko ma su fada aji kan kawar da dukkan wani 6acin rai ko ji ko ganewa kansu abin kunya daga ‘ya’yansu maza da mata. Sannan kuma iyaye talakawa kan yi amfani da wannan tsarin aurar da ‘ya’ya mata da wuri don su sauwaqewa kansu dawainiyarsu ta ciyarwa, suturtasu, kula da lafiyarsu da kuma daina damuwa da halayyarsu akan dukkan lamura na yau da kullum.

Su kuma ma su kudi, wannan ba abu ba ne da kan sa su damuwa ba, tunda akwai hali da yalwar da za su iya kula da ahalinsu baki daya da ma wasunsu. Shi ya sa ba kasafai su ke gaggawan aurar da ‘ya’yansu ba. Kuma in har za su aurar da su, toh sai sun nuna isa da gadara, su kuma gindaya wasu sharudda na babu gaira babu dalili wajen ba da ita ga wanda zai aura. Wannan fa bacin sun tabbatar da cewa ba talaka ba ne.

Ana irin wannan rayuwa ne fa ilimin boko ya shigowa al’umar Hausawa, a inda shi wannan salon ilimin babu abinda ya ke son tabbatarwa sai bai wa mutum walau mace ko namiji, babba ko yaro, mai arziki ko talaka, mai mulki ko wanda ake mulka, baqo ko dangari da dai suaransu samun ‘yancin kai ta hanyar koyar da shi ko ita yadda ake sarrafa rayuwar duniya ta kowane fanni.

Da shigowarsa cikin al’umma nan take Bahaushe ya gano illarsa ta koyawa yara fandarewa al’adunsu da kuma bata tarbiyar da aka san Hausawa da su kaka da kakanni. Kuma sai ta kasance cewa ilimin boko ba ya banbancewa tsakanin yadda ‘ya mace da d’a namiji su ke gudanar da rayuwa, sa6anin addinin Musulunci da ya fito ya yi tsari dakidaki na yadda namiji da mace za su gudanar da sha’aninsu na rayuwa.

Akwai ci gaba a kashi na biyu (2)

(c)2017 DesignWorld INT’L/SWS.Comms

A Kiyaye Dukkan haqqin Mallaka

https://web.facebook.com/DWinternational/

Comments

comments