WAYON ACI, WAI AN KORI KARE… 2

0
658

WAYON ACI, WAI AN KORI KARE DAGA GINDIN ‘DINYA (2)

Wannan ya na daya daga cikin dalilan da su ka sa Bahaushen mutum ya kyamaci ilimin boko a karon farko har ya dinga yaqi da ma su son su saka yaran Hausawa a cikin makarantun boko. Daga baya dai, ‘yan kalilan daga cikin wadanda su ka samo wannan ilimi na turawa ‘yan mulkin mallaka wanda da shi ake gudanar da rayuwar zamani, bacin  sun kammala sun samu manya manyan muqamai, sai sauran al’umma su ka haqura su ka fara sallamawa.

Toh fa kar ku manta Musulunci ya yi tanadin yadda ya kamata mace ta aiwatar da rayuwarta. Aure kuwa ya na daga cikin mafi tasiri wannan al’amari don tsaftaceta  da kuma al’ummar da ta fito daga ciki. Kuma kamar yadda bayani ya gabata, aurar da ‘ya mace a yayin da ta fara jinin al’ada izuwa kololuwar balagarta ya na daga cikin abinda addinin ya shar’anta, domin wa su daga cikin dalilan da aka bayana a baya.

Sai dai kash wannan tsarin ya samu akasin cin karo da tsarin neman ilimin boko ga ‘ya mace. Shi ilimin boko an shirya shi ne daki-daki kusan kusan kashi biyar, in an hada da rukunin farko na yaran da ba’a dad’e da yaye su daga sha nono ba wato abinda turawa ke cewa Nazare, inda yara kan yi shekara daya zuwa biyu a cikinsa.

Daga wannan mataki sai yaro ko yarinya su shiga makarantar furamare tsawon shekara shida. Bayan wannan sai su shiga makarantar sakandare karama da kuma babba inda a kowanne za su yi shekaru uku-uku wato wasu shekaru shida ke nan. Bacin sun gama za su sami takardar shedar kammala wannan mataki.

Da wanna shaidar gama karatun sakandare za su yi jarrabawar samun damar shiga jami’a a inda kowa zai zabi irin sana’ar da ya ke so ya iya a rayuwarsa ko rayuwarta. Anan akan yi fama na tsawon lokaci daga shekaru hudu zuwa bakwai, ya danganta da irin fannin harkokin rayuwa da dalibi ko daliba su ka za6a. Bacin sun kammala ne sai a ba su shaidar kammala karatun digiri na farko.

Toh fa da zarar matasan nan su samu wannan sheda ko kwalin ida digiri, sun kuma je sun yi wa kasarsu hidima na tsawon shekara guda cur, sai wata hukuma wacca aka tanadar aka kuma dora mata alhakin gudanar da wani tsari na samawa matasa gurbin aiwatar da abinda su ka koya a zahirance da ake kira NYSC a turance, sai ta ba su takardar shedar sun ba wa kasarsu gudummawa daga ilimin da Allah Ya ba.

Baya da wannan, sai a kama neman aiki. Maza da mata kowa ya kama fafutuka. Mai uwa agindin murhu kafin ka ce kwabo duk sun samu aiki a gudarare daban-daban, kama daga gwamnatin tarayya da na jihohi da kananan hukumomi zuwa masana’antu, kamfanoni ma su zaman kansu da dai sauransu. Wasu kuwa sai dai su kirkiro aiyuka da kansu su kama yi don gudun zaman kashe wando, wanda wasu kanyi har na tsawon shekaru da dama.

Ga duk mai hankali da tunani ya lura da kyau, wannan tsarin ya riga ya raba yara daga kusanci, kulawa, tarbiyar da ja a jika da iyaye kan yi wa ‘ya’yansu ta hanyar tafi da yaran daga gaban iyayen na tsawon lokaci a kullum. Don haka batun sa ido da mai da hankali kan lamuran yaro ko yarinya a harkokinsu na yau da kullum ya kan zamewa iyaye abu mawuyaci. Ba kamar daa ba inda da zarar d’a ko ‘ya sun yi wani abu ba’ko nan ta ke iyaye za su tsawatar ko su yi kwa6a.

Kuma saboda iya karatu da rubutu, da kuma koyo wasu abebad’e na rayuwar zamani sai ka ga yaran na yi wa iyayensu kallon wa su kauyawa ko gidadawa. Tun iyayen na tambaya yaran na yi mu su dariya har ta kai su haqura su yayewa kan su tozartarwa da ‘ya’yan su kan yi mu su. Daga nan kuma sai tsoron yi wa yaran magana ya shigo ciki rayuwarsu. Wannan shakku kuwa ba ‘ya’ya maza kawai ba har su ‘ya’ya mata. Kusan sun ma fi tsoron yi wa yara matan magana.

Wai maimakon yara su kama koyawa iyayensu sabbin abubuwan da su ka koyo idan iyayen ba wadanda su ka yi karatun boko ba ne, wato su ware wani lokaci na musamman don koyawa mahaifi ko mahaifiya yadda ake karatu da rubutu, wanda hakan ba qaramin kore jahilci zai yi daga al’ummarmu ba, a’a. Sai ka ga wadannan yaran su na gudun iyayen su san me duniya ta ke ciki, wasu har da nuna fushi da bacin rai in iyayensu su ka fiye yin tambaya don neman sani.

To fa yadda yaro ko yarinya ta dauki mahaifinta wawa-wawa ko mahaifiyarta wawiya-wawiya don saboda ba su da ilimin boko, toh hakan su kan dauki duk wani a cikin al’ummarsu muddin bai kai su ilimi ba, ko ya fi su wani matakin da su ke kai ba. Ka ga kuwa in mace ce, ai zai yi wuya wani wanda ke matsayi daidai da ita ko bai kai ta ba a ilimance ya ce zai gaya mata ta ji ko ta yi. Balle ace ta samu aiki mai ysoka wato za ta iya ci da kanta, ta tufatar da kanta daga irin aikin da ta samu bacin kammala karatun boko, ai zance ya qare.

Ku lura da kyau, wannan shine daya daga cikin dalilan da ya ke sa maza jin shakkar auren ‘ya mace muddun aka ce ta yi karatun boko har ta kai matakin kammala jami’a. Don kuwa sau da yawa neman wannan ilimin ya kan sa a kau da yarinya ko yaro daga gaban iyayensu a kai su makarantun kwana, kama daga na sakadare har izuwa jami’a. Kai wasu ma har a turasu kasashen waje su kadai ziqau ba tare da wani mai kwa6a ba. Sai kaga yarinya dududu ba ta kai shekaru ashirin ba a turata ita kadai wata duniyar da sunan karatun boko.

Sannan akwai abokan karatu da su kan ganewa idanunsu irin fantamawa da bad’alar da ake yi tsakanin samari da ‘yammata a makarantun kwana kama daga na sakadare har izuwa jami’a, ballema ace an tafi wata kasa ta daban don neman ilimi. Aikata sa6o, masha’a, iskanci da makamantansu da akan yi da ‘ya mace a ire-iren wadannan makarantun kwana, wanda dalibai kan shedawa idanunsu sau da yawa ya na sa su kyamar auren ‘ya mace wacca ta gama digiri daga jami’a komai kama kanta kuwa.

Kuma sau da yawa cudanya da wasu abokan zama, ‘kawayen huld’a ko karatu 6atagari, marasa kunya ya kan yi tasiri akan yaro ko yarinya wajen ajiye tarbiyar iyaye, koyawar addininsu da kuma uwa-uba tsoron Allah wajen sa su gudanar da ayyukan sa6o kamar su sace-sace, shaye-shaye, nuna tsiraici, halartar taron shagala da lalacewa, zinace-zinace, luwad’i da mad’igo, yin dabanci, shiga kungiyoyin tsubbu da sihiri don samun abin duniya da dai ire-irensu. Kafin su dawo ga iyayensu kuwa sau da yawa halayarsu ta sauya fiye da yadda ba’a ta6a zato ba.

Shi yasa mafi akasari su kansu ‘yan boko ba kasafai za ka ga sun aurin ‘yar boko ‘yar uwarsu ba. Sun gwammace su nemi yarinyar da ta kammala sakadare amma ba ta soma karatun a mataki na gaba ba su aura. Alabashshi ta dora karatun daga gidan mijinta bayan wani dan lokaci. Kuma ana samun hakan, amma fa sai wajen wanda ya fi matarsa ilimin bokon. In kuwa ba haka ba, sau da yawa sai ka ga matsalar raini na biyowa baya tsakanin miji da matarsa.

In ku na biye da wannan duba, za ku ga iyaye talakawa aurar da ‘ya’yansu mata wata hanyace wacca ta ke kawowa ire-iren wadannan  mutane sauqi a rayuwa. Ba don abinda za su samu daga ‘yarsu ba, a’a. Daga kai wadannan ‘ya’ya mata gidajen mazajensu da sigar aure ma ya isa. Don kuwa ko ba a samu komai ba ciyarwa, tufatarwa, wanka, wanki, kula da lafiya, samar da wajen zama da ma wa su buqatun yau da kullum da uba zai samar duk sai aga sun kau.

Mijin wannan yarinya shi ne zai dauki dukkan wadannan dawainiyar. Ka ga ko ba komai ai an samu sauqi. Toh idan kuma aka ce akwai yara mata 2, 3, 4 ko fiye a gaban irin wadannan iyaye, toh su fa ala kulli halin su na tattare da wannan tararrabi na yaya za su yi da wadannan ‘yammata ma su bin juna agufi agufi. Wato daya na bin daya da balaga sun ha66ake sun zama gindima-gindiman mata, wa su har budurcin su ya soma zubewa an rasa inda za’a sa su tunda dama gidan ba yalwatacce ba ne. Irin na rufin asirin nan ne kawai.

Sabanin haka a gidan ma su kudi da wadata, in an samu irin wannan yanayin, su kan tura yaransu maza da mata yin karatu ala tilas, ko yarinya na son karatun ko bata so. Sau da yawa mawadata babu ruwansu da abubuwan da addininsu wato Musulmin da akasin haka, ya shinfida. Duk abinda zai faru su na gadarar kudi zai yi maganinsa. Wai yarinya za ta dauki cikin shege ba abin damuwa ba ne a wajensu ba. Abinda kawai su ka yi imani da shi shine in dai yaro ko yarinya za su yi karatu, toh fa an gama.

Wai yaronsu zai dirkawa wata ciki, ba su dauke shi komai ba. In yarinya ce akwai damar da za’a kai ta asibiti a kawar mata da wannan matsala ba tare da jinkiri ba. In yaro ne kodai su ce sam ba shi ba ne ko kuma su samu lauyoyinsu su yi barazanar tuhumar yarinya da iyayenta da cewa sun yi wa dansu kazafi har su nemi ci wa uban wannan ‘ya mutunci. In kuwa su ya su ne, toh kar ta san kar sai a nemi yin sulhu. In ta yi tsamari kuwa, sai su yi wuff su tura yaro Turai a nemi shi a rasa.

Bacin an kawar da matsalar sai kowa yayi wa dansa ko ‘yarsa kashedin a kul su ka qara bari hakan ta sake faruwa tsakaninsu. Zancen aure a wannan yanayi babu shi ko kadan. Za kuma su nuna mu su muhimmanci yin karatu har ma su tambayi yaran a wace kasa su ke son su je yi karatun a wata siga ta toshiyar baki. Yaro ko yariya ta fadi inda ta ke so, a nema mu su makarantar, a kuma turasu uwa-uba duniya ko da kuwa ba su da dangi iya balle na baba a can.

Zancen addinin shari’ar Islama ta yi hani da tafiyar ‘yarinya wani gari babu muharrami ai wannan na kauyawa ne don mafi yawancinsu ba su san komai game da addininsu ba. Su dai su san su Musulmi ne kawai. Don haka duk inda aka ce su yi bayanin wane addini su ke yi, sai su ce ko su cike a fom din cewa addinin Mususlunci. Kai in su ka ga abin ma zai kawo mu su wani cikas, toh kawai sai su yi gum da bakinsu tun da mafi yawancinsu ba sallah su ke yi ba in sun fita kasar waje.

Toh yaron da ya fita wata kasa, ba shi da ilimin addininsa, babu wani magabaci mai fada a ji, ga kudi ana turo masa akai akai, ga rayuwa ta cudanya tsakaninsa da ‘yammata tsala-tsala kuma kala-kala daga dukkanin jinsin bil Adama, ga quruciya, ga abokai da ‘chiku na ambaliya sha’awa, ga kwalisa, ga gari da yanayi da wuraren jin dadi iri-iri da samun biyan buqata ta kowane fanni ba dare ba rana, ga shaidanu su na kai-kawo, su na hure ma sa kunne ala ayya halin, fisabililLahi ta yaya za a ce yaron nan zai kai da bantensa.

Toh, cire wannan yaro ka maye gurbinsa da ‘ya mace. Ta fuskanci dukkan irin wadannan damammaki koma fiye a wata kasa da babu kowa na ta sai dai labarinsu. Ai kuwa duk mai hankali zai san cewa sai an yi da gaske za a samu qanzo-qanzo daga cikin halaiyatta ta gari daga gareta. Bayan ta dawo gida, wanne irin rayuwa ake ganin za ta zo ta gudanar a gidan wani wai shi ne mijinta, da zai juya ta yadda ya ke so. Ai kowa ya san wannan abu ne da zai yi wuya auren gurguwa daga nesa.

Kar kuma ace wai irin wannan d’abi’a daga mace mai digiri sai wad’anda ba a gaban iyayensu ko kuma daga gidansu su ka yi ba, a’a. Kusan duk kanwar jaa ce. Sai dai a gaskiya wadanda su ka fi wuyan sha’ani su ne matan da su ka yi karatu a waje. Don kusan  da yawansu ba sua ma iya dawo da hankalinsu ko tunaninsu gida har su nemi yarda a auresu a nan. Mafi akasarinsu rayuwa a nan ta kan yi mu su qunci, saboda ba sua samun sake da walwalar da su ka saba da su a Turai ko Amurka ko inda su ka je karatu.

Amma in har ta kama dole su dawo gida fa, toh sau da yawa za ka sami ire-iren wadannan mata tunaninsu ya chanja matuqa. Za ka samesu da zaqewa, feleqe, gadara-gadara, fuffuka, jan aji, ‘karya, rainuwa, kushe, da yawan qorafi da qosawa akan komai na rayuwa. Tunda kuma a gidan wadata ta ke, akwai isassun dakuna da kowa zai bararraje ya sakata ya wala, ba tare da ta fuskanci takura ko tsangwama daga kowa ba.

Sannan a irin wannan gida ga abinci mai nagarta, sutura na qawa, kayan alatu, motar hawa, bukukuwa daban-daban kai har da fita kasar waje yawon buda ido akai akai. Yau a na wannan kasa gobe a na wancan gari duk iyaye na samarwa rid’a-rid’an ‘yayansu maza da mata. A irin wannan rayuwa ta holewa ba tare da mutum yasan ciwon nema ko yadda ake juya d’ari ya koma kwabo ba, sai ka samu yara ‘yammata uku, hudu, biyar ko ma fiye a gidan wani attajirin da ba’a san ma su na nan ba.

Kuma sau da yawa, sai an yi dace za ka samu an aurar da yarinya a gidan ta zauna a gidan mijinta. Ba dan komai ba sai don wadatar mijin ba kasafai ta kan kai ta uban yarinyar ba. Saboda haka zuwan yarinya gidan mijinta kamar wani koma-baya ne a rayuwarta. Mace kuwa kowa ya sani ‘yar hutu ce. Duk sanda aka ce ga wani abu wanda zai rage mata wani jin dad’in da ta saba, ta wadata da shi, toh fa dole za’a samu rashin jituwa da wannan yanayi. Shi ya sa mafi yawaancin auren ‘yan gidan ma su wadata ba ya qarqo.

Sabanin wannan al’amari idan daga gidan talaka aka auri yarinya ta tashi daga wani matsatstsen daki guda daya da ta ke kwana da kannenta su biyu ko uku ta koma wani gida mai dakuna biyu kowanne da bayan-gidansa, ga na kar6ar baki, ga wajen cin abinci daban, kana ga madafa wadatacce har da rumbun ajiye nau’in abinci kalakala, sannan a qara mata da tsakar gida da shuke-shuke a ciki duk ace na ta ne. Ai kaffa-kaffa za ta dinga yi da barin wannan ni’ima ta koma wannan akurkin da ta baro a gidan uban.

Sannan a lura da kyau, shi ma uban wannan ‘yar talaka, abin farin-cikinsa ne daga cikin ‘ya’yansa mata hudu ko biyar ace guda daya ce rak ta ke gabansu, ita ma don ba ta gama riqa ba ne. Wasu daga cikin yayyenta na gidanjen mazajensu su kadai, wasu kuma a matsayin mata ta biyu ko ta uku ko ta hudu ta ke a gidan mijinta. In dai yarinyar ta ce ta ji ta gani ta na son mijinta, toh fa barin gaban iyayenta shi ne mafi a’ala a rayuwarta.

Akwai ci gaba a kashi na uku (3)

(c)2017 DesignWorld INT’L/SWS.Comms

A Kiyaye Dukkan haqqin Mallaka

https://web.facebook.com/DWinternational/

 

Comments

comments