KYAKKYAWAR BUDURWA MAI GEMU…

0
291
 TA SHIGA KUNDIN TARIHIN DUNIYA
KYAKKYAWAR BUDURWA MAIGEMU
Harnaam Kaur
Daga Ahmadu Manaja Bauchi
 
img-20161020-wa0007 A wani sabon rahoton hukumar ajiyar abubuwan tarihi na duniya “Guinness World Records” a bana, sun bayyanar da wata matashiya mai shekaru 24 a duniya, a matsayin wadda ta lashe kambun shekarar 2017.
 
Harnaam Kaur, ‘yar asalin kasar Birtaniya, wadda take da yawan gashin fuska kamar namiji, ta bayyanar da labarin ta, a matsayin wani abun da ta sha wahala, domin kuwa idan aka ganta da gemu da gashin baki, sai a dinga tsokalanta.
 
Haka ya sa ta shiga cikin damuwa, amma daga bisani ta dauki cewar, wannan wata baiwa cimg-20161020-wa0009
e da Allah yayi mata. Tun tana ‘yar shekara goma sha biyu 12, ta fara gemu, a wannan lokacin ne aka duba lafiyar ta, aka gano cewar, jikin ta yana dauke da wani sinadari dake hana fitowar gashi a jikin mata, ita nata yana da karfi, don haka gashi zai dinga fitowa a jikin ta kamar namiji.
Tun dai a wannan lokacin ne ta daina yanke gashin fuskar ta, yanzu haka dai gashin nata yakai tsawon zira’I ko a ce inci shida 6.
 
A yayin wani bukin nuna kawar kaya, Harnaam, ta gabatar da kanta a matsayin mace da tafi yawan gashi a tsakanin mata, hakan ya jawo hankalin mutane da dama a kasar Ingila.
img-20161020-wa0011
Ta bayyanar da cewar, wannan baiwa ce daga Allah, don haka kada wani ko wata su raina irin baiwar da Allah ya yi musu a rayuwa. Hasalima sai su gode mishi, domin yanzu gashi ta shiga cikin tarihin duniya.

Comments

comments