DILLALAN FILAYE A ABUJA SUN KOKA

0
166
DILLALAN FILAYE A ABUJA SUN KOKA
Taswirar Birnin Tarayyan Najeriya Abuja

Rahoton Ibrahim Babangida Surajo

Sana’ar dillancin filaye a birnin tarayya Abuja tana daya daga cikin sana’o’in da su ke garawa a ‘yan shekarun baya baya nan, saboda romon da ake samu a cikinta wadda hakan ya sanya har wasu su ke yi mata lakabi da sana’ar ‘Dare daya Allah kan yi Bature’.

Tabbas wannan sana’a ta amsa sunanta tare la’akari da yadda za ka ga dillali a jiya yana fadi tashin jerangiya a kafa da ‘yan takardun filaye a hannunsa, amma kashegari in Allah Ya yi masa gyadar dogo ya yi ‘Hitting’ kamar yadda su ke fada wato ya samu ya sayar da wani fili, sai kawai ka yi aune da shi ya gwangwaje a cikin katuwar mota ta zamani ya na alfarma kamar kanin sarki. Wato shi ma ya shigo gari ya bi sahun manyan mutane.

Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da yadda filaye da gidaje su ke dan karen tsada a birnin Tarayya da kewayensa. Ta yadda mallakar muhalli a wannan gari sai dai wane da wane. Dillalan kan samu kazamin kudi ne ta hanyar cajin mai saye ko sayar da fili abin daya kama daga kashi biyar zuwa kashi goma cikin dari na jimillar kudin da aka sayar da hajar.

DILLALAN FILAYE A ABUJA SUN KOKA
Babban Masallacin Abuja

Bayanai sun nuna fili ko gida a birnin Tarayya Abuja ya fi tsada akan fili ko gida a birnin Newyork na kasar Amurka. Wannan irin kamshin dangoma da kasa take yi a birnin na Abuja ya samo asali ne tun fiye da shekaru ashirin da suka shude ta inda manyan ma’aikata da ma su hannu da shuni su ka shiga gasar ganin sun mallaki muhalli kama daga wanda za su zauna da iyalansu, har ya zuwa gidajen haya da kasuwanni na zamani da aka fi sani da suna Plaza.

Filaye da gidaje a Abuja sun kara samun tagomashi a cikin shekaru sha shidda da suka gabata, wato tun bayan da mulkin damokuradiyya ya zauna daram da gindinsa. Manyan ‘yan siyasa, kama daga ‘yan Majalisu da kuma Ministoci hankalinsu ya karkata wajen kokarin sayen filaye da gidaje a Abuja don gogayya da junansu wajen kokarinsu na ganin sun mallaki abin duniya ta ko wane hali.

Bincike ya nuna cewa biliyoyin kudin da wadannan ‘yan siyasa su ke amfani da su wajen sayen kasa a Abuja, kudade ne da ake zargin ko dai an karkatar da su kai tsaye daga aljihun gwamnati ko kuwa su na daya daga cikin kudaden da su ke karkatarwa daga cikin kudaden da aka dora ma su amana don gabatar da wasu ayyuka na musamman ga al’ummomin da su ke wakilta.

To koma dai yaya abin yake, canjin gwamnati da aka samu a kasa a halin yanzu ya yi matukar shafar wannan sana’a kwarai da gaske ta yadda har ta kai ga da yawa daga cikin dillalan su na kokawa ganin yadda wannan sana’a ta su ta cushe kuma ta tsaya cik. Wanda hakan ya sanya wasu daga cikinsu ma sai dai abin da suka tara a baya suke ci a yanzu.

DILLALAN FILAYE A ABUJA SUN KOKA
Ofishin Hukumar Kula da Sadarwa ta Kasa

A ta bakin wani dillalin fili mazaunin gari Abuja da DWi ta zanta da shi wanda kuma baya son a ambaci sunansa ya sheda mana cewa “Sabon salon wannan sabuwar gwamnatin a karkashin jagorancin Shugaba Buhari na ‘Ba ni ci kuma ba ni bari kowa ya ci’ shi ya sanya babu ma su kudi a kasa, ba labara ba wadanda za su iya canke kudi su sayi fili ko gida a halin yanzu a Abuja.”

Ya ci gaba da cewa “Ko dai da ya ke mu yanzu gafiya ta tsira da na bakinta, amma tuni ni na fara lalubo wata sana’a da zan koma in zuba kudi in fara domin kasan an ce wai zara bata barin dami. Wato kudi komin yawansu idan dai ba juya su ake yi ba, to kuwa za su kare.”

Har wayau ya kara bayani da cewa wadanda ma suke boye da kudade a gidajensu a halin yanzu tsoro suke ma su fito dasu tsaba, domin sayen wata kaddara ta daruruwan miliyoyi domin gudun kada dakarun hukumomin yaki da cin hanci da rashawa su kai masu bara. Ko kuwa su samu wata hujja ta yi ma su dirar mikiya.

Da na sake tambayarsa ko wace sana’a yak e shawarar komawa? Sai ya kada baki yace “Ina tunanin komawa gona ne. Wato badi in mu na da rai in samu wata kadada in shuke ta da Citta ko kuma Ridi don sayarwa ga kamfanoni masu bukata.”

Da yake amsa tambayar da na yi masa dangane da ko yana jin su kadai ne wannan abu ya shafa ganin yadda jama’ar kasa ke karaji saboda yadda aka shiga matsin rayuwa a wannan shekara sakamakon tattalin arzikin kasar Najeriya da ya samu targade saboda faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya da kuma faduwar darajar Naira?

Sai ya ce “Ko da yake mu masu sayen hajarmu ba masu yunwa ba ne, amma dai na tabbata wannan ya shafe mu ne a fakaice saboda yadda jikkatar tattalin arzikin kasar ya tilasta hukumomin gwamnati kara tsuke bakin aljihunsu da kuma toshe ramukan beraye. Kuma a wannan bangaren ina zaton bayan mu akwai ma su sayar da motoci a nan Abuja a cikin wadanda su ke jin jiki.”

DILLALAN FILAYE A ABUJA SUN KOKA
Hukumar Al’adun Gargajiya ta Najeriya

Da na ziyarci daya daga ciki matattara ta dillalan filaye wacce take a Unguwar Area 11 da ke a cikin gundumar Garki a garin Abuja na samu hada-hadar wannan wuri ba ta da karsashi kamar a ‘yan watannin baya inda za ka ga dillalan su na ta shige da fice zuwa cikin hukumar Tsarawa da kuma tantance filaye a garin Abuja.

Wanda koma da bayan hakan na samu babu yawan jama’ar da aka saba gani a wurin, sannan kuma ‘yan kadan din da su ke a wurin su ke a zaune suna hira ne da karatun jarida.

Ibrahim B. Surajo daga FCT Abuja

(c)2016 DWi

Comments

comments